Annabi (saww) mai gaskiya abin gaskatawa, Mai Taqama da wahayin Ubangijin talikai, Shi da kansa ya amsa mana wannan tambayar acikin wani hadisi.
Ga abinda yake cewa :
"ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALICCI ALJANU NE BISA NAU'O'I GUDA UKU:
1. Akwai nau'in da suke bisa siffar Macizai da kunamu da dabbobin Qasa.
2. Akwai kuma nau'in da suke bisa kamar Guguwa acikin Iska.
3. Akwai kuma nau'in da su akwai Hisabi da Ukuba akansu.
KUMA ALLAH YA HALICCI MUTANE MA ABISA SIFFOFI GUDA UKU:
1. Akwai wasu nau'in da suke kamar dabbobi. Allah yana cewa : "ZUCIYA GARESU AMMA BASSU FAHIMTAR (GASKIYA) DA ITA. KUMA SUNA DA IDANU AMMA BASSU GANI DASHI, KUMA SUNA DA KUNNUWA AMMA BASSU JI DASHI".
2. Akwai kuma nau'in da Jikkunansu irin na Bil-Adama ne amma zukatansu irin na Shaitanu ne.
3. Sai kuma nau'in da Zasu kasance acikin inuwar Allah aranar da babu wata inuwa sai tasa.
Acikin wani hadisin kuma Manzon Allah (saww) yace:
"ALJANU KALA UKU NE. 1. AKWAI WADANDA SUKE DA FUKAFUKAI SUNA TASHI ACIKIN ISKA. 2. AKWAI KUMA NAU'IN DA SUKE MACIZAI NE DA KARNUKA. 3. AKWAI KUMA NAU'IN DA SUKE SAUKA AWAJE (SU ZAUNA ZUWA WANI LOKACI) SANNAN SU TASHI".
DAGA ZAUREN FIQHU. DON QARIN BAYANI ADUBA:
– KITABUL AZAMATI na Abush Shaikh.
– ALMJRUHEEN na Ibnu Hibban juzu'i na uku shafi na 107.
– KITABUL HAWATIF na Ibnu Abid Dunya, shafi na 156.
– JAMI'US SAGHEER na Imam Suyutiy, hadisi na 2,838.
– SAHIHUL JAMI'I na Albaniy. hadisi na 3,109.
Bisa Hujjah da dalilai daga hadisai da dama, wannan yana nuna mana hadarin dake tattare da Jifan karnuna da maciza ba tare da hakki ba.
Lallai mu guji yin haka. Domin kuwa watarana za'a gamu da abinda ba'a zato. (Allah shi kiyayemu).