Adalci a mahangar Musulunci yana da bambanci da yadda abun yake abisa tunaninmu.
Ita kalmar adalci, ma'narta shine AJIYE KOWANNE ABU BISA MUHALLINSA. Ba tare da nuna bambanci ko fifita wani bangare, ko Qaskanta wani bangare ba.
Adalci ga al'ummar Musulmai ba ya yiwuwa dole sai Shugabanninsu sun kyale komai sun koma zuwa ga littafin Allah da Sunnar Manzonsa (saww).
Ta wannan hanyar ne Shugaba da mabiyansa da Ma'aikatansa duk zasu kasance tamkar tsintsiya, madaurinsu guda, Kuma tsawonsu guda. Babu nuna fifitaka, ko goyon baya ga wani bangare don chutar da wani bangare.
Kuma kowanne mutum za'a biyashi hakkinsa daga asusun gwamnati Gwargwadon wahala ko Muhimmancin aikinsa. Kuma kowanne mai laifi za'a hukuntashi Karkashin hukuncin Allah da Manzonsa (saww) gwargwadon nauyi ko munin laifinsa.
Amma irin wannan adalci zai yi wahala Shugabanni su iya aikatashi awannan zamanin da muke ciki, kuma awannan Qasar tamu Nigeria wacce take da rinjayen Musulmai, amma take Iqirarin bin kundin tsarin Mulki wanda mutane suka zauna suka rubutashi bisa Ma'aunin ra'ayinsu na DEMOKRADIYYA...
Sai dai muyi fatan Allah ya shiryemu baki daya, kuma ya taimaki Shugabanninmu ya ganar dasu gaskiya kuma y as basu ikon aiki da ita.