SUBHANALLAH!! Zan baku labarin wani abu ne wanda ya faru jiya da daddare.. Zan baku labarin nan ne Amatsayin gargadi ga matasa. ba wai don ALFAHARI ba.
Jiya bayan Maghriba na dawo daga Makaranta sai ga wasu mutane a mota.. Sukayi sallama dani, bayan na fito sai suka fito da wani Saurayi daga Mota...
Sun daukoshi kamar gawa, ko motsi ba ya yi... Da na tambayesu menene ya sameshi? Sai suka ce Wai yaron yaje wajen Match ne (gasar buga kwallon kafa). Sun tsaya acikin Daji zasuyi fitsari sai suka ganshi an cirashi sama.... Shi ba a Qasa ba, kuma shi ba chan sama ba.
Yana ta eehu.. Sai da suka zo suka rikeshi sannan ya fado Qasa.. daga nan kuma ya suma. Gashi nan kamar matacce.
Da nazo na fara karanta masa Ayoyin Tuhumar Aljani, sai ya farfado, ya fara eehu yana Qokarin guduwa.. Wato Aljani ya bayyana ajikinsa kenan.
Da na tambayi Aljanin kamar haka:
Z/F: BISMILLAHI wanene? wa ke tare damu?
ALJANI: Sunana Abdullahi.
Z/F: Menene addininka?
ALJANI: Ni musulmi ne.
Z/F: Menene dalilin shigarka jikin wannan yaron?
ALJANI: FITSARI YAYI MIN ACIKIN BAKI NA!! Nayi alwala zan tafi Masallaci, sai ga yaron nan ya dawo daga Wajen wasan Kwallo, yazo ya Wa atsa min ruwa sannan yayi min Fitsari acikin bakina..
Shi yasa na bayyana agareshi. na firgitashi, kuma nayi niyyar in daukeshi in tafi dashi inda har abada ba za'a taba samunshi ba!!
Dama ina jin haushinsa.. Rannan yazo diban yashi acikin kogin yana kokarin dukan wani Bijimi, sai bulalar ta sameni.. Sai kuma yau yazo ya Qara yimin wani laifin.
*****************
Zan turo cikakken Audio Recording din acikin ZAUREN FIQHU WHATSAPP in anjima kadan. In sha Allah.
Gargadin da zan yiwa matasa 'yan kwallo (harma wa anda basu yin kwallon) anan shine: Ku rika kulawa da ambaton Allah cikin dukkan abinda zakuyi.
Ku rika neman tsarin Allah daga dukkan sharri aduk lokacin da zaku tsuguna fitsari agida ko a Daji. ko amakaranta.
Da ace wannan saurayin yayi addu'a kafin ya tsuguna, tabbas da wannan aljanin bai ganshi ba.