Mayakan Boko Haram sun hallaka dakarun kasar Kamaru biyu a lokacin wani gumurzu a kan iyakar kasar da Nigeria.
Lamarin ya auku ne a karshen mako a lokacin da dakarun Kamaru ke rangadi a garin Zelevet da ke arewacin kasar.
An kashe 'yan Boko Haram su uku a lokacin arangamar.
A makon da ya gabata ma 'yan Boko Haram sun hallaka mutane 20 a wasu kauyuka da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.
Kasashen Nigeria da Nijar da Kamaru da kuma Chadi sun kafa dakarun hadin gwiwa domin yaki da Boko Haram.
Title :
Yan Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru
Description : Mayakan Boko Haram sun hallaka dakarun kasar Kamaru biyu a lokacin wani gumurzu a kan iyakar kasar da Nigeria. Lamarin ya auku ne a karshen...
Rating :
5