Wasu rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na cewar wasu 'yan bindiga da ake sa ran 'yan Boko Haram ne suna kai hari a kusa da birnin.
Wata majiya ta tsaro ta shaida wa BBC cewa sojin Najeriya na ci gaba da kokarin fatattakar maharan.
Wasu bayanai na cewa 'yan Boko Haram din na kokarin shiga Maidugurin ne ta wani yanki da ake kira 'Cashew Plantain' da ke bayan barikin sojoji na Giwa.
Su ma wasu mazauna birnin na Maiduguri sun shaida wa BBC cewar suna jin karar tashin bama-bamai da bindigogi ta ko'ina.
Mutane kuma na ta guje-guje don tsere wa lamarin.
Yayinda wasu dalibai a jami'ar Maiduguri ke cewar an umurce su da su kwanta a kasa.
Hukumomin tsaro a birnin sun ce, sai nan gaba za su yi karin haske kan lamarin.