TAMBAYA TA 1596
*******************
Assalamu alaikum.mallam barka da kokari Allah yasaka maka da mafificin alkhairi .dan Allah mallam Ina da matsalane jinin al,adane wata biyu be zoba yanzu kuma yau kwana biyu se naga wani abu bakikkirin kamar zan fara al,ada ya zubo. har yanzu kuma yana zubowa shine nake so ayi mini bayanin zanyi sallah ne ko inbari seya dauke?.aboye sunana. Allah ya taimaka. dan Allah a amsa min, sannan dan Allah inason numbar wayarku. Allah ya saka da alkhairi abisa fadakarwa da ake mana.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa Rahmatullah.
Shi irin wannan abun. Idan yazo miki acikin lokacin da kike sa ran zuwan jinin al'adarki, to zaki daukeshi ne amatsayin jinin al'ada.
Amma idan yazo miki be awani lokaci dabam, ko kuma bayan kinyi wankan tsarki, to wannan ba zaki daukeshi abakin komai ba.
Akwai ruwaya daga Ummu Atiyyah (ra) - wata sahabiya ce- tace sun kasance (azamanin Annabi a.s.) bassu daukar wannan irin wannan abakin komai. (Wato wannan mai kamar kalar Hanta din nan kenan, ko kuma mai kama da gurbataccen jinin nan).
WALLAHU A'ALAM .