TA YAYA ZAKI WA MIJINKI BIYAYYA (003) . Wallafar jamila muktar saleh. . ** TARIHIN MAWALLAFIYAR ** . JAMILA MUKHTAR SALEH an haife ni a unguwar kafar bai a shekara 1989. An sanyani makarantar firamare ta kayalwa watau ( Ahamdu comassie modal science primary school) kadan daga cikin malaman mu sune malama bailkisu, malama Rukayya muhammad da sauransu, Allah yasakanya masu da aljannah firdausi, Ameen. . A shekara ta 2002 na samu nasarar shiga makarantar kwalejin yan mata dake katsina watau GOVT.GIRLS, COLLAGE KATSINA ( GGCK). Kadan daga cikin malaman mu na wannan makaranta a wannan lokaci sune; mal. Jamilu, mal. Babangida, da sunransu Allah yasakama masu da Aljannah firdausi Ameen. . Nasamu wucewa zuwa kwalejin koyon harshen larabci da ilimin Addinin musulunci watau (ATC) a shekara 2006. Kadan daga cikin malaman mu na wannan makaranta sune; mal. Ashiru Bala yandaki,mal. Masa'udu, da sauransu. . Allah (SWT) yasaka masu da Aljannah firdausi Ameen. . Bayan kammala wannan makaranta ATC sai na samu aikin koyarwa a wata makarantar islamiyya mai suna TARBIYYATUL AULAD dake kofar bai a shekarar 2007. Kasantuwar makaranta ce mai son cigaban Addinin musulunci, kuma sunada kyawawan manufofi, kadan daga cikin irin manufofin wannan makarantar na cigaban Addinin musulunci sune; . 1) Tarbiyyantar da dalibai a karkashin jagorancin AL'QUR'ANI DA HADISAN ANNABI SAW. 2) isar da sakon Allah kuma umurni da kyawanan ayyuka da kuma hani da munanan ayyuka, DAs. A shekara 2011 nafara kokarin wallafa wani littafi dan takaitacce; domin isar da sako ko umurni Annabi (saw) da yake cewa . " BALLIGU ANNI WALAU AYA" . ma'ana (ku isar sakona ko da aya dayane ). . Na fara buga wannan littafi ne mai suna; . TA YAYA ZAKI WA MIJINKI BIYAYYA? na hausa da fatan zai amfani al'ummar musulmi baki daya. . In an samu kuskure a gyara mani manufa shine alkhairi, Allah yake shiryar da wanda ya so.