TAMBAYA TA 1597
******************
Assalamu alaikum warahmatullah malam Allah ya saka da mafificin alkhairi ameen Dan Allah malam ka taimaka min da wata addua wacce zan dinga yi saboda naje asibiti anyi min BTL amma daga baya sai malamin MU yace nayi kuskure saboda bani da wata kwakkwaran hujjan dazan tsayar da haihuwa . to wallahi malam nayi nadaman yin hakan har na koma asibiti akan awarware aikin sai sukace bazai yiwu ba Dan Allah malam a taimaka min da yadda zanyi aboye sunana na gode. Dalibar ka mai biyayya.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Babbar mafita agareki ita ce Ki yawaita istigfari. Tun da Manzon Allah (saww) yace: "DUK WANDA YA YAWAITA ISTIGFARI, ALLAH ZAI SANYA MASA MAFITA DAGA KOWANNE QUNCI... "
Amma babban kuskurenki shine rashin tambayar Malamai akan matakin da ya kamata ki bi. Domin bai halatta ga duk wani Musulmi ya aikata wani abu ba, har sai ya san hukuncin Allah acikin wannan abin.
WALLAHU A'ALAM.