Swansea ta ci Arsenal kwallo daya mai ban haushi a gasar Premier da suka yi ranar Litinin a filin wasa na Emirates.
Bafetimbi Gomis ne ya ci kwallon da kai sauran minti biyar a tashi wasa daga bugun da Jefferson ya yi wo masa.
Da wannan sakamakon Swansea ta takawa Arsenal burkin yawan lashe wasanni 11 da ta yi a jere.
Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na uku a teburin Premier yayin da Manchester City wacce ke mataki na biyu a teburin ta ba ta tazarar maki uku tsakani.
Arsenal za ta ziyarci Manchester United a gasar Premier ranar Lahadi a Old Trafford.