WANI BABBAN ABIN MAMAKI GA shakira kuma takasa daina kallon dantala yadda kasan wanda aka makale mata wuya ahaka,
wadda tunda shakira tai wayo taxo duniya sannan tagirma tafara mallakar hankalin kanta bata taba kallon wani namiji wanda ya mallaki hankalin kansaba daidaida na secon 5 ba batareda data kauda kantaba saigashi yau takalli wani wadda akalla sunfi second goma suna kallon juna gabadayansu babu wanda yadauke kai.
Daga bisani kuma shakiran tadawo cikin hayyacinta sannan taysauri tadauke kanta,
amma duk dahaka haryanzu kirjinta dukan uku uku yake saikace wadda taga mutuwarta ita kanta abin yabata mamaki matuka,
shin me yake shirin afkuwa agarenine?
Kodai wannan mutumin mugum mutum ne shiyasa naji ina faduwar gaba da ganinsa,
ta tambayi kanta saidai matsalar bata da amsoshin tanbayan dataima kanta danhaka dole tai shiru.
Abangaren dantala kuwa shikansa abin ya girgizashi duk dacewa dantala mutum ne mai farin jini dakuma kwarjini sannan mata kyawawa sunsha nuna masa so dakauna agareshi amma baitaba jin wacce nan take azuciya ya amince da itaba nan take sai wannan kyakykyawar budurwar dayagani yanzu,
zuciyarsa ta dakamasa tsawo tareda fadin cewa agareshi kai shashasha baka da hankaline yar gidan masu kudicefa koso kake kasaka kanka cikin bala in dabakasan karshensaba.
To wannan budurwar dakake gani tafi karfinka talaka dakai kawai,
aikuwa nan take ya rungumi shawarar da zuciyarsa tabashi sannan lokaci guda suka fara kokarin saukowa daga saman kan ginin dasuke aikin zuwaga wajansu salen.
Idanda za a tambayi dantala ta wanne tsanin yasauko acikin tsani biyardin dasuke wajen tofa saidai akashehi dan lokacin dayake saukowa gabadaya zuciyarsa cike take da tunanin wannan yarinyar daya gani.
Cikin nutsuwa kodayaushe kamaryadda yake yakaraso wajen fiskar nan tasa sai fitar da wani kyakykyawan murmushi takeyi wanda koda yaushe bata rabuwa dashi.
Salamun alaikum yai sallama awajen
gabadaya aka amsa sallamar har 'yan matan biyun sannan shakiran
takalli fiskar dantala tace ga wannan daga manaja yace akawo muku ku raba kuyi hakuri rashin lapiyanshne yatashi.
Dantala yamika hannu biyu cikin girmamawa yakarbi kudin gamida cewa Allah yabashi lpy.
Wannan abu dayai ba karamin burge shakira yaiba lokaci guda kuma kawai saitaji gabadaya komai nasa burgeta yake sannan yasaki wani tattausan murmushi agareta yace
Allah sarki nida nake yaro karami da anbawa yayuna aida rabon zaifi kyau ko.
Shakira taymurmushi tace aiba mu muka zabekaba yayinnakane suka zabeka.
Yajuyo ya kalli 'yan aikin yai murmushi yace toshikenan tunda kun amince dahakan,
sannan shakiran tace toshikenan mu zamu barku mutafi sai anjima.
Sannan 'yan matan 2 suka jiyo sun a tapia cikin nutsuwa kadanne daga cikin 'yan aikin suka iya juyarda kansu suka kalli wani gun amma mafi yawancinsu sun raja a akallon kyawawan yan matan.
Lokacin dasukahau mota shakira tadan waigo wadda adaidai wannan lokacin shima dan tala yadan waigo aikuwa karaf sai aka hada ido cikin sauri suka kauda kawunansu sannan zahra taja mota suka wuce.
Kai dantala nifa ban yardaba kaga wani kallo da wannan yarinyar takema kuwa anya kuwa bata kyasaba kuwa dannaga alama akan fiskrata,
amma gsky indai hartanaso tomun warke wlh kaga idan ka aureta kudi kawai zamu samu shikenan kakarmu tayanke saka.
Wannan furucine da sale yayi bayan sun gama raba kudin sun koma gida yayin dama suke shirin yin bacci.
Cikin tsawa dantala yacewa sale kai sale wai bakada hankaline kaikenan arayuwarka idan bakai zancen kudiba bakada abin fadi waikai me kadauki duniyane haba.
Sannan ita wannan yarinyar karyane nibawani kallona datake.
Towai idanma kallon nawa take dame zan aureta kokuwa dashekaruna?
Koko a a kataba ganin inda akai aure mutum bashida aikinyi.
Sannan kadinga tunani amaganarka sale wannan yarinyar dakake gani tafi karfina dan daganinta kasan yar gidan manyan mutanece ba 'yan gidan talakawa irinmuba dan haka ba riwana acikin wannan maganar taka.
Yana gama maganar yajuya masa baya yakwanta daya bangaren,
babu ruwanso dakudi ko matsa yi mallam indai harson nagaskiyane
sale yafada gamida tsaki.
Dantala baikara cewa komaiba saidai kawai kwakwalwarsa datake zayyano masa fiskar shakira azahirin gsky shikansa yasan yakamu dason yarinyar daya gani to amma iya imaninsa dai yasan tafi karfinsa dan haka gwara kawai yahakurar ma kansa ita yashare.
Tunlokacin dasuka rabuda 'yan aikin shakirama babu abinda ke yawo acikin zuciyarta sai hoton dan tala, bakin kuwa saimaimaita sunan kawai yake yafi akirga dan bata kaunar ta manta sunan kosaudayane arayuwarta.
Abin bai girmamaba sai lokacin dataje gun bacce nanfa bacce yaki yiwuwa sannan lokaci guda kuma fiskar dantala tadingamata gizo acikin dakin.
Sai anan shakira ta tabbarma kanta tabbas takamu da wani abu wanda ake kira waishi SO....