A JINGINE YAKE Ajikin motarsa, wata rantsatstsiyar prado, yayi wankan manyan kaya saifaman kamshin turare yake ita kanta hular ba abarta hakaba saida aka hadata da kayan dayafi dacewa da ita ajikinta.
Tundazu daya sauka agidannasu yaketa goge goge da gyare gyare saikace wanda kura tagama bulewa, wankan yayi masa kyau sosai dan azahirin gsky duk yarinyar data ganshi awannan kyakykyawan wanka gamida kallon kyakykyawan surar matashin saurayin dolene ta kyasa.
Ya dubi agogonsa akalla minti ashirin dakiran yarinyar tun farko daya faka a harabar gidannasu amma haryanzu taki fitowa.
Tawani bangarem kuma tausayin kansa yake ganin yadda yakamu da soyayyar yarinya lokaci guda amma haryanzu yakasa samun damar mallakar zuciyar yarinyar.
Yarasa wacce irin macece shakira duk irin dabaru da kuma salo na samari dazai yariga yayi amma haryanzu yakasa shawo kan yarinyar tasoshi kuma a iya saninshi yasan cewa shakira bata dawani saurayi to amma maiyasa bata sona,
.yatanbayi kansa yayin dayai zurfin acikin tunanine yaji zazzakar muryarta taratsa kunnuwansa da sallama cikin sauri yadago kai tareda da amsa sallamar gamida kallonta.
Duk dacewa bata fara a da zuwansa sannan babu ko alamar murmushi akan fiskarta amma ahakan kallon dayayiwa shakira saiyaga tbbs babu ko jayayya takara kyau.
Ina wuni mas 'ud tafada cikin sanyi fuskarta nanuna alamar kamar atakure take.
Lpy lau yay saurin amsawa gamida sakin wani tattausan murmushi agareta.
Shima kansa wannan murmushin bai tasiriba domin haryanzu fiskar shakira ayadda tazo ahaka take.
Haba shakira wannan shanyar taki ai tadade da bushewa tundazu nakiraki amma saiyanzu karfa kimanta nabaro wasu abubuwan sosai sabida mahimmancinki nazonan kinga kuwa ai bancancanci hakaba,
sannan a iya sanina ni babban masoyinkine tbbs ina tutiya dahaka amma maiyasa haryanzu nakeyi tuntube da matsaloli daga gareki mas ud ne yayi wannan furucin.
Saidai kayi hakuri ina wani aikinne tafada sannan tadan juyar dakai da alama harta fara kosawa da hirar tasu.
Babu komai shakira koda kinyi laipi sama da wannan zan iya yafemiki aikin wuce wannan agurina,
to amma mukarasa cikin falo mana dan Abbama yasan nazo ai.
Dasauri shakira tajuyo dakai tace a a dan gsky yanzuma sauri nakeyi saloon zan tafi kayi hakuri mas ud banida lokaci saida kadawo wani lokacin nagode sai anjima
bata saurari abinda mas ud zai fadaba tafada cikin gidan gabadaya kan mas ud yadaure yarasa wacce irin yarinyace shakira gashi Allah yajefeshi da kaunarta amma haryanzu takasa fahimtarsa.
Bisa dole yashiga motarsa yafita daga gidan yauma kamar kullum babu kwarin guywa.
Tana shiga ta gamu da abban nasu afalo dayake wannan satin yana gida tambayar dayafara yimata shine ya baki shigo da mas ud din cikiba.
Cewatayi yace sauri yakene akwai inda zashi.
Kyaleta kawai yayi amma yasa karya take dan yasan ayanda mas ud yake son shakira bazai iya hira da ita nadan wannan kurarren lokacinba.
Kedaiki fadi gskydai kodai korarsa kikayi shakira, danni narasa wannan wacce irin yarinyace,
yaro mai hankali da girmama mutane amma yarinyarnan sai yawo takemasa da hankali.
Mahaifiyarta tai wannan furucin lokacin da take fitowa daga bangarn wajenta zuwa cikin falon.
Dasauri shakiran ta dubeta gamida fadin a a haba umma aikinsan bazan muku karyaba sannan tai saurin tashige dakinta tana zuwa tafada kan gadonta.
Daga gefen zuciyarta wani haushin mas ud takeji ita kwata kwata bata sonshi kuma tarasa yadda za ai tasoshi.
Wannan wacce irin rayuwace da ace ana dasa so azuciya dakuwa tabbs data dasa na mas ud kodan tafarantama iyayenta amma bazata iyaba kai wannan wanne irin lamarine haka yake bayyana agareta.
Shakira ita kadaice mace a 'ya'yan Alhaji abdullahi wato abbansu saimaza guda 2 wadda duka suna waje suna karatu da usman da shakir wadanda duka yayintane itadinma danta dage cewa anan nigeria takeson yin karatu shiyasa abban nasu yabarta dan duk abinda shakira takeso to abbanta da ummanta suma sunaso.
Mahaifinnasu babban mai kudine sosai shahararren dan kasuwane wanda ya ke harkar atamfofi da shadduna dadai sauran kayan suturun mata haka ya bunkasa sosai dan har akasan sama mutane da dama suna ciyar da iyalansu sosai.
Mutumin kirkine sannan akwai sanin yakamata kuma bashida wulakata mutane.
Tana cikin dakinnatane taji sallamar zara babbar kawarta daga falo
bayan sungaisa da abba da ummanta zaran take tanbayar shakira sukace mata tana cikin dakinta
Aikuwa tana shigowa suka rungume juna cikin farin ciki kamar wadda ba jiya jiyannan suka rabuba
Shakirance ta dubi zara tace ke lpy naganki kamar da damuwa atattaredake naga kamar bakya farin ciki sosai
Wlh shakira kedai bari wai abbane yabani kudin kingansu dubi darine yace wai naje nasallami yan aikin rufin sabon gidanmu dazamu koma.
Kinji dan Allah wai ina macena dani wainice da sallamar yan aiki.
A ah tokuma ina manajan yake?
Bashida lpy wai ciwon cikin sane yatashi dan Allah sakira kintsa kirakani mutafi wlh kunyama nakeji naje nikadai.
Nex Part 3.