Lokacin da mutuwa ta riski annabi Musa Alaihis Salam, sai ya roki Allah ya kusatar da shi Baitul Makdis.
Abu Huraira ya ce: Ma'aikin Allah ya ce: "Da ina wajen, da na nuna muku kabarinsa a gefen hanya karkashin wata jigawar jar Kasa". Bukhari (3407) da Muslim (2372).
An ruwaito daga Wahab Ibn Manbahi: Mala'iku ne suka bisne shi da ma yi masa sallah, kuma yai shekaru 120 a duniya.
Alaihis Salam.