Manchester United ta amince da yarjejeniyar dauko dan kwallon PSV Eindhoven Memphis Depay a karshen kakar wasan bana.
Kudin da United din za ta dauko dan kwallon zai kai fam miliyan 25 zuwa 30, a inda zai taka leda har zuwa kashen kakar 2019 da kuma zabin zai iya kara shekara daya.
Likitoci za su duba lafiyar dan wasan mai shekaru 21 a mako mai zuwa, zai kuma koma United ne da zarar an bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa a Junin badi.
Depay wanda ya buga tamaula karkashin Louis van Gaal da tawagar kwallon kafar Holland, yana daga cikin 'yan wasan da PSG da Liverpool suka yi zawarci.
source bbchausa.com