Ba wani bane yafadi hakan, nine nafada, kuma na fajimci hakanne ta hanyar dogon bincike da nazari danayi akan ibadar tattaki. Sannan inada yakinin duk wani mai kyakkyawan tunani bazai sabawa maganar tawa ba.
A yan kwanakinnan ne yan shi'a suka tafi wajen garin zaria a kasa domin ibadar tattaki.
Ance wai lada ake samu, in an mutu a hanya ma shahada akayi, Allahu akbar! Kaji ibada mai falala!
Sai dai duk matsayin jihadi a musulunci an daukewa yara kanana, an daukewa mata da duk wani mai rauni. Saide naga su iyalan Khomainin duk basu dauke ba, toh wai ko tattaki yafi jihadi falala da daraja ne???
Ita kanta hijira akwai nau'in wadanda wajabcinta ya fadi akansu, amma banda babbar ibada wato TATTAKI.
Saide duk falalarda wanna ibada ta tattaki take dashi duk mabiyan addinin shi'a sune suke kwashewa, domin kuwa shu imamin nasu na najeriya zama yake a garinsa suje su same shi, kenan shi bayayi. Kenan bai samu ladan ibadar ba.
Sai naga cewa idan za'ayi wani abu na izala ba a garin shugaban izalar akeyiba, misali; rabonda ayi wa'azi a Yola anfi shekara, Mal. Kabiru dan Gombe ne, har namanta rabonda aje gombe wa'azin kasa. Ai hakan yafi dacewa da adalci ko???
Toh ni dai dan karamin yaro ne, ban sani ba ko akwai wani ma wanke wannan dattin. In akwai FAL YATAFADDAL MASHKURAN MA'AJURA.....................
Awaisu Al'arabee Fagge