Akwai wani mahaukaci yana bara cikin kasuwa amman duk wanda yabashi sadaka sai ya ce:
"KAYIMA KANKA".
To akwai wata mata bata bashi sadaka amman tana jin haushin abin da mahaukacin yake fada.
Wata rana ta kirashi ta hada masa lemo tabashi, ashe tasa masa guba, domin yaci yamutu, sai ya karba.
Mai makon yayi mata godiya sai yace:
"KINYIMA KANKI"
Ya juya yai tafiyarsa.
A zuciyarta sai tace:
"Nayiwa kaina ko?"
Daga yau bazaka sake gayawa wani haka ba, saita kwashe da dariyar mugunta.
Bayan mahaukacin yatafi sai yahadu da wasu yara yan makaranta sukace masa.
"KAYIMA KANKA Yau ba wani abu da kasamo wajen bara kabamu ?
Yunwa muke ji"
Sai yace "ba komai saidai wannan lemon da ban sha ba."
Yabasu sai sukace:
"Wannan kwanon kamar na mamanmu."
Sai yace:
"idan kun gama kukai mata kwanon."
Sai suka shanye suna ta murna suka taho gida.
Koda zuwansu ta hangi kwanon a hannunsu sai tafara cewa ina kuka dauko kwanon nan ?
Sai su kayi mata bayani.
Daga nan har mai afkuwa ta afku.
Tsokana.
=======
Saboda haka shuka ALKHAIRI, Idan ba haka ba, kaima kayiwa kanka.
Mahaukacifa yayi gaskiya ko kunga laifinsa ?
Allah yabamu ikon shuka alkhairi.
Domin kasancewa damu akoda yaushe.