Nasake duban tsohon.agogon dake daure ahannuna wanda tun zamanin ina aji biyu asakandire na siye shi, Karfe bakwai da minti talatin agogon yanuna min, yayin da alokaci' guda kuma nasake kankame lemar dake hannuna wacce iska take baraxanar dauke ta, sakamakon hadarin daya taso, yacanxa launin garin gaba daya, ya koma bakikkirin kamar dare yayi. Wanda hakan yahaifar da karancin ababen hawan dake xirga-zirga akan titin danake tafiya, wanda hakan yasa narasa abinda xan hau domin xuwa makaranta. Raina yafara baci ganin lokacin dana bata ina jiran mota amma ban samu ba, gashi kuma lokaci sai kara wuce yake kuma na tabba indai malamin yashiga aji to babu wani dalibi da ya isa yasake shiga, Hakan kuma bakaramin matsala xai iya janyomin ba, kasancewar malamin gwanine wajen daukan duk sunayen daliban da suka halarci ajinsa aduk lokacin daya gama basu darasi. Wannan ne dalilin dayasa dalibai suke mutukar daukan lokacin darasin sa da muhimmanci. Gashi yanzu hadari yana kokarin hanani karasawa makaranta akan lokaci. Duk da cewar nayi nisa sosai da gida amma da akwai sauran tafiya daga inda nake xuwa makarantar, Kuma gashi mintuna Talatin kawai suka ragemin kafin Malamin yashiga aji. Yayyafin daya fara sauka akaina ahankali ne yasa nadawo daga duniyar tunanin dana tafi, da sauri nafara kokawar bude lemar yayin da iskar dake tasowa take kokarin hanani bude lemar, domin kare kaina da kuma takardun karatuna jikewa da ruwan. Dakyar natattaro duk karfina nasamu nasarar bude tsohuwar lemar wacce samanta yafara yagewa sakamakon tsawon lokacin data dauka aduniya tana shan rana da kuma dukan ruwan sama. Haka naci gaba da tafiya cikin ruwan hannuna daya kankame da lemar yayin dana dafe takarduna da daya hannun, duk da lemar dana sa hakan bai hanani jikewa ba, sakamakon kofofin dake samanta tako ina, sai dai koba komai dai ta taka muhimmiyar rawa wajen bawa takarduna kariya daga dukan ruwan saman. Ahaka naci gaba da tafiya zuciyata cike da sake-saken ina ma nima ina da mota kamar yanda sauran abokan karatuna suke da su, kaga da babu ruwana da tafiya ruwa yana jikani. Ruwan saman daya barke kamar da bakin kwarya shi ya dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi, ayanzu kam na tabbata babu abinda xai hanani shan dukan ruwan saman,Cikin sauri nafara tunanin inda yakamata naje na fakewa dukan ruwan, daga can nesa na hango wata rubabbiyar rumfa wacce rabinta ke xubar da ruwa, mutane biyu ne tsaye acikin rumfar sun kurawa ruwan da yake zubowa daga sama idanu kamar suna kokarin Kirga adadin ruwan da yake xuba. Na sunkuya nafara tattare kafar wandona, danufin kaucewa jar kasar data jike da ruwa agefen titin da nake tafiya. Na taka burki atsakiyar titin, yayin dana juyo cike da mamaki da kuma bacin rai. Nakalli kayan dake jikina farar T.Shirt da) Blue din Jeans wadanda nake matukar ji dasu acikin kayana, amma alokaci guda sun koma jajawur kamar nayi wanka acikin kwababbiyar jar kasa. Raina yayi kololuwar baci yayin dana juya naga yanda takarduna sukayi filla-filla acikin ruwan dake gudu atsakiyar titin. Najuya nasake kallon inda mai motar dayayimin hakan yanufa, ga mamakina sai naga motar tana dawowa da baya ahankali. Badan karnayi qaryaba da sai nace tun da nake kuma duk da kasancewata dan jami'a, ban taba ganin motar data tafi da hankali da imanina irin wannan motar ba. Duk da raina abace yake akan abinda mai motar yayi min, amma hakan bai hanani sha'awar motarba. Ina tsaye kikam kamar gunki acikin ruwan har motar ta tsaya daf dani................Zanci gaba