TAMBAYA TA 1600
*******************
Assalamu'alaikum! Malam barka da warhaka, Allah yakara basira ameen.
Dan Allah malam ina bukatar shawarine bisaga wata damuwa danake ciki, matsalar kuwa itace: na kasance mutum mai karancin ilimin addini wanda koda rubutun ajami bana iya karantawa, saboda hakan yasa ina son zuwa daukar karatu amma se ina shakkar tunkarar malamin da kudirin yaja min baki kuma ya fassara min. Dan Allah malam shine nakeson ataimakamin da shawarin yanda ya kamata. nagode
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Hakika Babu wani abin jin kunya ko kuma jin nauyi bisa neman ilimi. tun da abu ne wanda Allah ya farlanta maka kuma zai tambayeka akansa.
Manzon Allah (saww) yana cewa:
"NEMAN ILIMI FARILLAH NE AKAN DUKKAN MUSULMAI MAZA DA MUSULMAI MATA".
Shaikh Abdurrahman Al-Akhdhariy (rah) yana cewa: "farkon abinda yake wajaba abisa baligi (mutumin da ya kai shekarun balaga. namiji ko mace) Shine ya Kyautata imaninsa, Sannan ya san abinda zai kyautata farillansa na kansa dasu. Kamar sanin Hukunce hukuncen sallah, da na tsarki da na azumi".
To amatsayinka na baligi, ta wacce hanya zaka san wadannan abubuwan idan baka je wajen Malamai ba?
Shawara ana ita ce: Kayi kokari ka danne zuciyarka kaje wajen Malamin Fiqhu wanda ka yarda dashi, ka mika kanka da lokacinka da hankalinka gareshi. ka nemi ilimin addininka, ka sauke farillar nan da take kanka.
Ina fatan Allah yasa sauran Matasan da suke cikin zauren nan suyi koyi dakai.
WALLAHU A'ALAM.