TAMBAYA TA 1599
*******************
Assalamu alaykum ya mu'alleem, dft katashi lfy ya mai jiki ta kara ji? Dan girman Allah tambaya gareni mai mahimmanci Malan wata kanwatace take zaman idda kenan aurenta nabaya ne ya mutu kuma tanaso tasake wani auren amma ya kasance tana yin goyo babynta amma al,adarta bata zuwa harsai bayan tayaye sannan take zuwa dan Allah Malan ya bayanin iddarta take ayimana bayani koda acikin group ne Dan wasu su amfana nagode.
shin Zata iya yin wani auren batare da tayaye yaron ba?
(Daga Maman T)
AMSA
******
Wa alaikis salam wa Rahmatullah.
Hakika acikin Alqur'ani Allah ya riga ya bayyana mana yadda kowacce irin mace zatayi iddarta. kamar haka :
Acikin Suratul Baqarah yace:
"MATAYEN DA AKA SAKI, ZASU ZAUNAR DA KANSU TSAWON JINI UKU (WATO HAILA UKU KENAN).
Kin ga wannan ana magana ne akan wacce batta da ciki ko goyo kenan. Kuma shekarunta sun kai na yin hailar. har ma tanayi.
Acikin Suratut Talaaq (Ayah ta hudu) kuma Allah yace:
"WADANNAN MATAYEN DA SUKA FIDDA TSAMMANI GAME DA HAILA DAGA CIKIN MATAYENKU, (WATO TSOFAFFI WADANDA SUN DENA YIN HAILA) IDAN KUMA KOKONTO (GAME DA IDDARSU, TUNDA BASU YIN JINI) TO IDDARSU ITA CE WATANNI UKU. HAKANAN MATAYEN DA BASU TABA YIN HAILA BA. (WATO KAMAR QARAMAR YARINYAR DA AKAYI AURENTA, HAR AKA SAKETA AMMA SHEKARUNTA BASU KAI NA HAILA BA. - ITA MA IDDARTA WATA UKU NE).
"MA'ABOTA CIKI KUMA (WATO MASU JUNA BIYU) IDDARSU ITA CE SU HAIFE ABINDA KE CIKINSU (WATO DA ZARAR SUN HAIHU TO SUN GAMA IDDA KENAN)."
To kinga yadda bayanin iddah yake. duk acikinsu ba'a ware mace mai goyo ba. domin ita ma iddarta shine JINI UKU. Dole sai ta yaye yaronta, ta jira zuwan hailarta, tayi tsarki, sannan wata hailar tazo, tayi tsarki, da haka har sai tayi haila uku. Koda kuwa hailar tata batta zuwa sai bayan Shekara guda atsakani.
JAN KUNNEN DA ZANYI ANAN SHINE: Ita da take iddah, a ina ta samu Manemi (bazawari) har take neman fatawar yin aure, alhali kuwa tana cikin iddah??
Da yawa ana samun Matayen da suna cikin iddah amma suna waya da Bazawari ko saurayi, Harma sukan shirya maganar auren gaba dayanta. Wata ma da zarar ta kammala idda da sati daya ko biyu sai kaji tana daura wani auren.
Haramun ne Qulla maganar aure tun idda bata Qare ba. Dole sai anyi ahankali an bi dokokin Allah sau da Qafa idan ana neman dacewa aduniya da lahira.
WALLAHU A'ALAM.