Daga cikin Karairayin da mutane suke yi acikin zantukansu na yau da kullum, akwai NAU'I UKU wadanda Allah ba ya rubuta Zunubi ga masu yinta..
Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUKKAN WATA QARYA ANA RUBUTA (LAIFINTA) AKAN 'DAN ADAM. IN BANDA GUDA UKU:
1. MUTUMIN DA YAKE QARYA AWAJEN YAQI. (DON TSORATAR DA ABOKAN GABA) DOMIN KUWA SHI YAQI 'DAN YAUDARA NE.
2. DA KUMA MUTUMIN DA YAKE YIWA MACE QARYA DON NEMAN YARDARTA.
3. DA MUTUMIN DA YAKE YIN QARYA DOMIN YA SULHUNTA TSAKANIN MUTANE BIYU (WADANDA SUKE GABA).
- Ibnus Sunniy ne ya ruwaitoshi.
DAGA ZAUREN FIQHU
*******
# Number 1 da 3, duk wadannan ana yin qaryar ne don neman isar da wani aikin alkhairi.
# Shi kuwa number 2 fa wannan ba yana nufin cewa mutum ya rika yaudarar 'yan-mata yana zuwa da motocin aro, ko suturar aro don neman biyan bukatarsa.. A'a ana nufin mutumin da suka samu sabani tsakaninsa da matarsa, zai iya yi mata Qarya don neman sulhuntawa da ita..
Hakanan mace ma zata iya yiwa mijinta Qarya don neman yardarsa. Amma fa banda Qaryar da za'ayi don neman danne hakkin Abokiyar zama, ko kuma chutar da ita. Wannan bai halatta ba.
SHIN WACCE KA TA'BA YI ACIKIN KARIRAYIN NAN GUDA UKU?