Ma'aikin Allah ya hadu da wasu annabawan Allah a sama daga cikinsu akwai annabi Musa.
Ga yadda haduwarsu ta kasance: "Sai ya hau sama har sai da ya iso sama ta bakwai ya nemi a bude, sai aka ce: Waye wannan? Sai ya ce: Jubrilu ne. Sai aka ce kai da waye? Sai ya ce: Muhammadu. Sai aka ce: Shin an tura masa ne? Sai ya ce: eh! Sai ya ce: Maraba da shi madalla da mai zuwan da ya zo.
Yayin da na shiga sai ga Musa sai ya ce: Wannan ne Musa yi masa sallama, sai na masa sallama ya amsa sannan ya ce: Maraba da dan'uwa nagartacce kuma annabi nagartacce.
Da na wuce sai ya fashe da kuka sai aka ce masa: Me yasa ka kuka sai ya ce: Ina kuka saboda yaro da aka aiko bayana al'ummarsa za su shiga aljanna fiye da yawan wadda za su shiga daga al'ummata". Bukhari (3887), Muslim (162).
Hafiz ya yi bayanin abin da malamai suka ce, annabi Musa ba yayi kuka ne don hasada ba, Allah ya cire hasada a zukatan daidaikun muminai ballantana za6a66u a wajen Allah, wato annabawa. Abin da ya bashi takaici shi ne irin saba masa da Banu Isra'ila suka yi wadda ya janyo masa raguwar magoya baya duk da yawan shekaru da yayi cikinsu, saboda kowane annabi darajarsa na karuwa da yawan mabiyansa.
Sannan kuma kiransa da yayi da yaro ba kaskantar da shi yayi ba, ya fadi haka ne domin nuna kudurar Allah ta yadda ya daukaka mai kananan shekaru wajen daraja a kan wadda suka fi shi.