BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
tsira da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa da Sahabbansa.
Allah Ubangijin talikai yana cewa:
"(YA MUHAMMADU) IDAN BAYINA SUKA TAMBAYEKA GAME DANI, TO (KACE MUSU) NI INA NAN AKUSA. INA JIN KIRAN MAI KIRA IDAN YA KIRANI".
(Suratul Bakarah, ayah ta 186).
Acikin Suratun Namli ayah ta 62 Allah yana cewa:
"WANENE WANDA YAKE AMSA ADDU'AR MABUKACI IDAN YA KIRASHI, KUMA YAKE YAYE DAMUWA (ALLAH KENAN).
Manzon Allah (saww) yana cewa: "ADDU'A ITA CE (HAKIKAR) IBADAH".
(Sahihul Jami'i).
A wani hadisin kuma yana cewa: "BABU WANI ABU MAFI GIRMA AWAJEN ALLAH KAMAR ADDU'A".
(Sahihul Jami'i).
Sannan yace: "DUK WANDA YAKE SO ALLAH YA RIKA AMSA MASA YAYIN DA YAKE CIKIN TSANANIN BUKATA, TO SAI YA YAWAITA ADDU'A ALOKACIN DA YAKE CIKIN YALWATA".
(Sahihul Jami'i).
Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace : "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa:
"HAKIKA ACIKIN DARE AKWAI WANI LOKACI WANDA BABU WANI BAWA MUSULMI WANDA ZAI DACE DA SAMUNTA YANA ROKON ALKHAIRI ACIKIN LAMARIN DUNIYA DA LAHIRA, FACHE SAI (ALLAH DIN) YA BASHI ABIN. KUMA WANNAN HAKA YAKE AKOWANNE DARE".
(Muslim ne ya fitar da hadisin).
Kun ga wannan hadisin yana karantar damu cewa lallai mu dage sosai da addu'a da ibadah acikin kowanne dare domin neman dacewa.
Awani hadisin kuma, Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace: Naji Annabi (saww) yana cewa:
"ADDU'AR DA AKAYITA ATSAKANIN KIRAN SALLAH DA IQAAMAH, BA'A MAYAR DA ITA (Wato Allah yana karbarta kai tsaye).
(Targheeb).
Wannan hadisin yana nuna mana Muhimmancin yawaita ADDU'A a wannan tsakanin.
Awani hadisin kuma daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yana cewa:
Manzon Allah (saww) yace "MAFI KUSANCIN YADDA BAWA ZAI KASANCE ZUWA GA UBANGIJINSA MAI GIRMA DA DAUKAKA, SHINE ALOKACIN DA YAKE SUJJADAH. DON HAKA KU YAWAITA ADDU'A".
(Sahihut Targheeb).
Kun ga wannan hadisin kuma yana karantar damu Muhimmancin yawaita ADDU'A acikin sujjadah kenan.
Don haka sai mu yawaita sallolin bayan farillah wato nafilfili da rana. Sannan da dare ma mu yawaita nafilfili kamar yadda magabatanmu Sahabbai da tabi'ai da mabiyan bayansu, da sauran mutanen kwarai suka kasance suna yi.
A wani wajen kuma Manzon Rahama (saww) yace:
"MAFIFICIN ZIKIRI SHINE "LA ILAHA ILLLAL LAHU". KUMA MAFIFICIYAR ADDU'A ITA CE "ALHAMDU LILLAHI".
(Sahihul Jami'i).
Wannan yana qara fito mana da darajar kalmar nan ta Shahada kenan. Da kuma darajar kalmar nan ta godiya. Wato ALHAMDULILLAH wacce ka fadeta abayan kowacce ni'ima, Allah yati rantsuwa cewa sai ya Qara maka.
Anan zamu tsaya sai da dare kuma ko gobe idan Allah ya kaimu zamuyi karatun KITABUL KABA'IR.