«fitowa na 8»»
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
'Yar uwata karki karaya, wallahi ke kyakkyawa ce mai dadin kallo, mai dadin qamshi, mai dadin murya, mai dadin mu'amalla, komai naki dadine dashi.
Haka Allah yayi ki, duk daya saka miki rauni qasa da namiji, amma fa raunin nan naki shine qarfinki.
Domin babu wani da namiji da zai gagare ki, sabo da Allah yabaki sirrin juya zuciya kamar yadda yabawa namiji sirrin juya wani da qarfi, don haka babban taimakon da zaki yiwa kanki shine kiyi nesa da girman kai, kisan cewa kinada wannan qarfin koda yaushe.
Son suna da alfahari yana tafiyar da mutuncin mace.
Shiyasa in tanada sha'ani take binciko qasan akwati, amma a gida sai daurin qirji, ko tsohon riga wanda in za a shayar da yaro nono kota wuyan rigar ana iya finciko shi.
Idan mijin yanason yaga lalle a jikinta to yayi fatan sha'ani ya taso.
Buqatarta kowa yace tayi kyau alabashi mijin karya gani, idan ta qarasa wajen sauran matan tace:
"Su wane da wane sun cika kallo, saisu Qura maka ido har karasa yadda zakayi tafiya"
Bayan kuwa tagama hado shika-shikan tayarda hankulan maza, kuma tace ita wallahi ba tallar kanta take yiba.
Duk macen data kamu da irin wannan matsalar ba abin da zata iyayi domin mai gidanta, kuma zuciyarta zatayi nisa qwarai daga tunanin irin shigar da zata yiwa mutum Daya kacal alhali idan tafita mutane ne dayawa zasu yaba, mazansu da matansu.
Ashe mijinta tunda shi Daya ne sai a saka masa na maneji, ko kwalliyar ma ba dolene yariqa gani ba.
Mace tagari dukiyarta da iliminta da shekarunta basa hana tayiwa mijinta hidima, ina sha'awar matar da wata zatace:
"Mu sayi kaza"
Ita kuma tace
"Maigidana bayaso"
Ba wai tace
"Tabdijan zansha fada kuwa" .
Manufa ba tsoron fadansa take yiba, tsoron ta sayi abinda ransa bazai soba.
Yakike ganin Khadija (R.A) data auri mai gidanta (S.A.W) sai abin da yace za ayi!
Yakike ganin biyayyar da tayi masa duk da kasancewarta mai kudi shi talaka, amma ta saukar da kanta domin yi masa hidima har ta amsa kiran Rabbana ?
Yakike ganin saye zuciyar da tayi masa da har tsufanta zuwa rasuwarta bai da kamarta a zuciyarsa ?
Ke me zaisa bazaki kwatanta ba ?
Idan aka ajiye maganar daraja agefe guda.
Me Allah yabata a jikinta wande ke bai bakiba ?
Tafiki matsayi, amma ki karanta tarihi kiga qoqarin da tayi da zuciyarta da jikinta wajen tabbatar da mijinta a surar data rasu ta barshi.
Yi amfani da duk abin da Allah ya hore miki wajen biyayya ga mijinki.
Kiduba kigani Allah yayi miki halitta ta ban sha'awa wace dole a kalla, toki nuna masa, Yamiki murya mai dadi, toki jiyar dashi, Yabaki damar yin kwalliya kala daban-daban toki bar masa shi kadai, karki yarda wasu su riqa haduwa dashi a kanki.
BAN DA GIRMAN KAI.
Kiyi qoqari ki manta duk sifofin gidanku ko naki na kanki, kiyi tunanin irin sifar da kikeso mijinki ya sifantu da ita, da irin matsayin da kike so yakai.
Allah yabamu ikon yin aiki da abin da muke karantawa.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.