FARKON WADANDA ZA'AYI MUSU HISABI
Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Naji Manzon Allah (saww) yana cewa:
"Hakika farkon wanda za'a fara yiwa Hisabi daga cikin mutane aranar Alqiyamah shine wani mutum wanda yayi Shahada (wato ya mutu ayakin daukaka kalmar Allah).
Za'a fito dashi akawoshi. Allah zai sanar dashi ni'imomin da yayi masa, kuma shima zai sani.
Sannan Allah zai tambayeshi "SHIN MAI KA AIKATA DA WANNAN NI'IMAR?".
Sai yace : "Nayi ta yin Jihadi acikin addininka har sai da nayi shahada".
Sai Allah yace masa "QARYA KAKE YI. KAI DAI KAWAI KAYI YAQI NE DON ACE MAKA JARUMI. KUMA AN RIGA AN FA'DA".
Nan take Allah zai bada umurni a kifar dashi akan fuskarsa, arika jansa har sai an wurgashi acikin Wuta.
2. Sai kuma wani mutum wanda ya nemi ilimi, kuma ya karantar dashi. Kuma yayi karatun Alqur'ani sosai.
Za'a zo dashi sannan Allah zai tunasar dashi ni'imomin da yayi masa, kuma shima zai tuna. Sannan sai Allah ya tambayeshi "SHIN MAI KA AIKATA DA WANNAN NI'IMAR?".
Sai yace : "Na nemi ilimi, kuma na karantar dashi. Kuma na karanta Alqur'ani dominka.
Sai Allah yace masa: "QARYA KAKEYI!!! KAI DAI KAWAI KA NEMI ILIMI NE DON ARIKA CE MAKA 'MALAMI'. KUMA KAYI KARATUN ALQUR'ANI NE DON ARIKA CE MAKA 'MAKARANCI, KUMA AN RIGA AN FA'DA"
Sai Allah yasa a kifar dashi akan fuskarsa arika jansa har sai an wurgashi acikin wuta.
3. Sai kuma wani mutum wanda Allah ya yalwata masa arzikinsa, ya bashi kowanne nau'in dukiya. (kamar kudade, daloli, Motoci, gidaje, kampanoni, Jirage, Filaye, etc).
Za'a fito dashi. Sai Allah ya tunasar dashi ni'imomin da yayi masa, har sai ya tuna. Sannan Allah yace masa "SHIN MAI KA AIKATA DA WANNAN NI'IMAR?".
Sai yace : "Ban bar wata hanya wacce kake so aciyar da dukiya acikinta ba, fache sai da na ciyar (wato kamar gina Masallatai, makarantu, Raba abinci awatan Ramadhan, da sauransu).
Sai Allah yace masa : "QARYA KAKEYI. KAI DAI KAWAI KA AIKATA DUK WANNAN NE DON MUTANE SU RIKA CEWA 'KAI MAI KYAUTA NE'. KUMA AN RIGA AN FA'DA".
Sai Allah yayi umurni a kifar dashi akan fuskarsa arika jansa har sai an wurgashi acikin wuta..".
- Hadisi ne Sahihi. Yana nan acikin SAHIHUL AHADEETH ALQUDSIYYAH na Shaikh Mustaphal Adawiy.
DARASI
********
Hakika wannan hadisin yana da mutukar razanarwa ga duk wanda ya karantashi cikin nutsuwa. Kuma akwai darussa masu yawa acikinsa.
Zanso kowanne dalibin ZAUREN FIQHU ya gaya mana abubuwa guda biyu ko uku wadanda hadisin nan ya karantar dashi, sannan darussa guda nawa ka dauka/kika dauka acikin hadisin??