TAMBAYA TA 1603
*********************
Salama alaikum malam da fatan malam na cikin kochin lafiya tambayata ita ce muna yawan zuwa daji to indan muka tafi bamu samun salar juma'a to bayan ankare salar jum'ar mu muna iya yin jam'i domin gabatar da salar azahar ?malam dajin yakan iya kai wata uku kenan salar juma'a 12 kuma ance babu kiyawo mutum yarassa juma'a uku to yaya mu da muke rasa juma'a har 12?
AMSA
*******
WA ALAIKUMUS SALAM WA RAHMATULLAH.
Manzon Allah (saww) ya gaya mana muhimmancin Sallar juma'a acikin hadisai masu yawa, kuma ya tsoratar damu akan barinta ba tare da uzuri karbabbe ba.
Acikin hadisin da Imam Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar da kuma Abu Hurairah, Manzon Allah (saww) ya fada akan mimbarinsa cewa:
"LALLAI NE MUTANE SU DENA WULAKANTAR DA SALLAR JUMA'A. IDAN BA HAKA BA ALLAH ZAI SANYA RUFI BISA ZUCIYOYINSU, KUMA HAKIKA ZASU KASANCE DAGA CIKIN GAFALALLU".
Acikin wani ingantaccen hadisin kuma Manzon Rahama (saww) yace: "DUK WANDA YA RASA SALLAR JUMA'A GUDA UKU BA TARE DA UZURI BA, ALLAH ZAI SANYA RUFI BISA ZUCIYARSA". (WATO ZAI KULLE ZUCIYAR MUTUMIN YADDA BABU WANI ALKHAIRIN DA ZAI SAKE SHIGA CIKINTA).
Amma duk wannan ana magana ne akan wanda ya barta da gangan ba tare da wani uzuri ba. Amma in dai akwai uzurin Jinya, ko kuma tsoron faruwar wani abu, to babu komai.
Kace kuna zuwa daji ne. Shin babu wani gari akusa da dajin wanda zaku iya zuwa domin yin sallarku ta juma'a? In dai har akwai gari akusa, bai halatta ku zauna ku Qi zuwa ba.
Bisa mazhabin Malikiyyah in dai kun kai mutum goma sha biyu, kuma wajen da kuke din gari ne zaunanne to ya halatta ku tsayar da sallar juma'a.
A kula sosai da sallar juma'a kada Allah ya kama ka da laifin wulakantar da sallah.
WALLAHU A'ALAM.