Ma'aikin Allah ya ce: "Kar ku fifitani a kan Musa, mutane za su sume kuma sai na zamto farkon wanda zai farfado, sai ga Musa na rike da gefen Al'arshi, ban sani ba, yana daga cikin wanda suka sume amma suka rigani farkawa ko kuma yana daga cikin wadanda Allah ya toge". Bukhari (3408), Muslim (2373).
Wata rana Abubakar radiyallahu anhu suna ciniki da wani bayahude sai ya taya hajar bayahuden nan shi kuma ya ga kamar an yi masa tayin wulakanci sai ya ce: 'A'a ina rantsuwa da wanda ya fifita Musa a kan talikai baki daya. Wannan magana ta bata wa Abubakar rai, domin bayahude na nufin kowa ya shiga cikin wanda Allah ya fifita annabi Musa a kan su har ma'aikin Allah sai ya mari bayahude.
Bayahude sai ya kai karar Abubakar wajen ma'aikin Allah, sai ma'aikin Allah ya sanya aka kira Abubakar inda bayan shi ma ya fadi abin da ya hada su, sai ma'aikin Allah ya fadi abin da muka kawo a sama.