ARANAR YAQIN KHAIBARA wani kafiri ya sari Qafar Sahabin Manzon Allah (saww) mai suna SALAMAH IBNUL AK'WA'I.. Sai mutane suka fara kururuwa suna cewa :
"AN SARE QAFAR SALAMAH! AN SARE QAFAR SALAMAH!!"
Shi kuwa sai ya garzayo wajen Manzon Allah (saww) yayi nasa tofi sau uku awajen.. Nan take Qafar ta koma ta hade, bata sake yi masa ciwo ba.
- Imamul Bukhariy ne ya fitar da hadisin.
Ya Allah muna tawassuli da yawun bakin nan nasa mai tsarki, albarkacinsa ja warkas mana da zukatanmu, ka cire mana dukkan miyagun ayyuka, ka cika mana ita da tsantsar Soyayyar Sayyidul Awwaleena wal Aakhireen (saww).