Acikin kashi na farko mun kawo muku alamomi guda 37. Yanzu kuma insha Allahu zamu dora daga nan.
38. Za'a samu yawaitar SHAN GIYA (da sauran kayan maye)
39. Mutane zasu rika keta alfarmar Shari'ar Allah, suna aikata laifuffukan haddi, amma ba za'a iya tsayar musu da haddin ba.
40. 'Uwaye Mata zasu zama kamar abun banza agun 'ya'yansu.
41. Mutane Matalauta, masu tafiya tsirara, Marassa takalma zasu zama sune Masu Mulki da dukiya. Har zasu rika gasar gina dogayen gidaje.
42. Mata zasu shiga harkar Kasuwanci tare da mazaje.. Kafada-kafada.
43. Za'a samu Mazaje masu Kamanceceniya da mata. Wajen suturarsu, da yafiyarsu da maganarsu.
44. Za'a samu mataye masu Kamanceceniya da Mazaje awajen suturarsu da maganarsu da yafiyarsu.
45. Mutane zasu rika yin rantsuwa da wasu abubuwan banda Allah da littafinsa.
46. Za'a samu yawaitar Musulmai masu bayar da Shaidar Zurr. Koda ba'a tambayesu ba.
47. Mutane ba zasu rika yin sallama ba, sai ga wadanda suka sani.
48. Mutane zasu rika amfani da ilimin addini domin neman duniya.
49. Ayyukan neman lahira, za'a juyar dasu arika yinsu don neman samun abun duniya.
50. Masu Mulki zasu dauki dukiyar BAITUL MALI su mayar da ita tamkar dukiyarsu ta kansu.
Wadannan kadan kenan daga Alamomin tashin alkiyama wadanda Manzon Allah (saww) ya fadesu tun sama da shekaru 1,400 yace zaau faru. Kuma tabbas da yawa daga ciki sun faru kuma suna cigaba da faruwa ayanzu haka.
Wannan yana daga cikin alamomin gaskiyar Manzancinsa (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.