A kalla kimanin watanni biyu baya ya kamata wannan rubutu ya zo, amma bisa la'akari da cewa a lokacin al'amarin ya shafi rayuwar jarumar ne kawai sai mu ka yi shiru.
Akwai wata hira da aka taba yi da wani dan fim, abokin sana'ar jarumar, inda aka nemi ya fadi abun da ya sani game da ita, sai yace."Nafisa Abdullahi ta na da zafin soyayya, kuma shawarar da zan bata shine ta rage"
Bayan tarihin zazzafar soyayyar ta a baya, yanzu haka soyayyarta da wani edita mai suna ibrahim ita tafi daukar hankali a industiri.
Daga cikin abun da ya kambama soyayyar kuwa shine irin ganin da wadansu ke yi cewa nafisan ta girmeshi, sannan kuma, da mahaukaciyar soyayya da ta ke yi masa, sannan duk yanda ku ke da ita idan ka taba shi, sai an jiku da ita, kai a takaice har fim ta yi masa, domin ta lallaba shi.
To Amma me, daga bangaren shi ibrahim din kullum ya na wahalar da ita wannan jarumar ne, idan ya fito ta windo gobe sai ya ce sai ta rufin kwano zai fita, kun san dai namiji idan ya gane ana son sa.
Wani abu da ibrahim ya tsira shine kishi da duk jarumin da ya ga sun yi magana da jarumar ko da kuwa su na Aiki ne, a ranar sai ta wuni ta na lallashi, wannan abu ba karamin taba Career gwarzuwar jarumar 'yar soyayya ya yi ba.
To a jiya dai shi kuma baban soyayyar ya bulla a shafinsa na instagram ya na bayyana rabuwa da jaruma nafisa abdullahi, wai kawai don ta yi hoto da gogarman jarumin nan Adam Zango.
Ibrahim ya sa hoton nafi da adamu, wanda su ka dauka jiya lokacin da suke wani fim mai suna Kwamandan Mata. Inda yace. "Ya zama dole na rabu da ita, domin ta nuna ta zabe shi"
Mun ji wasu na cewa ban da abunka ai duk wani daukar fim ai akan yi hotuna, sannan wanda ka ke yi dashi ai bai san kana yi ba, sannan kuma da bai barta ba da watakila ba ku hadu ba.
To yanzu dai za mu sa ido duk wani sabon abu za mu kyankyasa mu ku, da wannan mu ke kira da wannan jaruma dafatan za ta rage zafin soyayyah.
@i_princeee @nafeesat_official