ssalamu Alaikum malam inafatan antashi lpiya malam munada tambayoyi guda biyu
1 malam takasance tanada cikin wata 3 sai ta wayi gari ta shiga ban daki sai cikin yazube sai taga wani abu kaman Dan kwado yafado bayan jinin yagama zuba saitasa tsintsiya ta share harda wnn abun maikama da kwado saitagaya wa mutane saisukace wai tayi kisan kai saitayi azumi 60 shine take Neman bayani kan wannn abun shin dagske ne ko kuma yaya? Dan cikin Allah ne yakaddaro da zubewansa ba ita tazubar ba shine take Neman bayani.
2. Malam nayi matukar nadama bisa ga kuskurenda nayi bantaba zuwa gun Malami ko boka ba saida Allah ya jarabeni da son wani mutum, Sai kawata ta ban shawara akan na kaisa gun malam ban taba zuwa ba sai ranar munje yaban carbi yace na dauki daya nadauka har sau 3 ya baiwa kawata itama tadauka sau 1 sai yayi ta rubuce rubuce akan wani faranti yana dauke da kasa yace nasaka hannu na abisan kasan nasaka bayan kwana 2 da zuwan mu gunsa sainayi bincike kan carbin da yaban yace nadauki daya sai akace man wlh dubace yayi Niko Allah yasani bansan dubace ba banma taba zuwa gun malam ba ko boka shine abun yadameni nayi matukar nadama akan zuwan danayi nayita istigfari akan Allah ya yafe man najene bisa ga kaddara to miye hukunci na Dan wlh INA bakin ciki da kuka aduk time dinda na tuna da wannan abun..
Daga wasu Mata bayin Allah.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
1. Wannan abinda ya faru, ba za'a kirashi da sunan KISAN KAI ba. Bisa dalilai guda biyu: Na farko ba ita ce ta zubar da cikin ba, ya zube ne bisa radin kansa.
Na biyu kuma bai fito da siffar rai ba. kuma ko motsi bai yi ba. Bisa dukkan alamu gudan jini be kawai. Don haka wannan babu wani Azumi sittin da zatayi.
Bai kamata mutane su rika kirkirar abubhwa acikin shari'ar Allah da gangan ba..
2. Hakika Manzon Allah (saww) yayi hani mai tsanani bisa zuwa wajen Bokaye ko matsafa ko 'yan duba. Kuma yace duk wanda yayi haka ba za'a karbi ibadarsa ba, har tsawon kwana arba'in. awata ruwayar kuma yace Ya kafirce ma dukkan abinda Annabi Muhammadu (saww) yazo dashi.
Amma kasancewar kinje ne bisa kuskure, bakiyi zaton haka yake ba, to muna kyautata raja'in cewa Ubangiji zai gafarta miki. Domin kuwa akwai hadisi ingantance daga Manzon Allah (saww) wanda yake cewa :
"UBANGIJI YA DAUKE MA AL'UMMATA SABODA NI, LAIFIN DA SUKA AIKATA CIKIN KUSKURE, DA WANDA SUKAYI CIKIN MANTUWA, DA KUMA WANDA AKA TILASTA MUSU AKANSA".
Sannan kuma kinyi nadama bisa laifinki. Kuma kince kina ta yin istigfari. Idan muka yi la'akari da yalwar rahamar Ubangiji bisa bayinsa, sai muga cewa in sha Allahu akwai kyakyawar fatan cewa Allah zai yafeki da gafararsa.
Ubangiji yana cewa : "KA GAYA MUSU : YA KU BAYINA WADANDA SUKAYI 'BARNA ABISA KAYUWANSU! KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH. HAKIKA SHI (ALLAH) YANA GAFARTA DUKKAN ZUNUBAI, SHI MAI GAFARA NE, MAI JIN-QAI".
Allah shi kiyayemu daga afkawa cikin hallaka. Allah shi bamu kyakyawan Qarshe.
WALLAHU A'ALAM.