shuru yayi bai sake magana ba, sai dai kakar tawa taci gaba to ku a wane gari kuka girma haka? Ya dakatar da ita, wannan tambayoyi duk basu taso ba, daman nayi ne na gwada ko kanta dai dai yake ba zararriya bace, to amman naga bata da alamun rashin lafia, baiwar Allah nidai ban san daga ina kike ba, ban kuma san wa ya kawo ki nan gidan ba, amman bani da wani da mai suna Aminu kuma kinga dai ni ba wani abu gare ni ba balle in ce kwadayi ya kawo ki, amman tunda bakuwa ce ke, na baki damar ki zauna a gidan nan har ki gano inda yanuwan ki suke, har ya mike nace Dan Allah ka tsaya Wallahi wallahi shi ya kawo ni nan gidan ya fadi mani kai ne mahaifin shi yama ce zai je wurinka,
mu jira shi ya dawo ai zai dawo daukar mu. Ya girgiza kai ya wuce ya fita, nan na ci gaba da zama shiru shiru ba mahaifina har dare yayi, haka muja kwana gidan nan. Bayan gari ya waye mun karya sai kakana ya leko muka gaisa, yace baiwar Allah gashi dai wanda kika ce har yanzun bai zo ba, anya ba karya yayi maki ba? Lokacin na sanya kuka domin na rasa ina zan saka kaina, na kuma nanata masu ni nan yace mani gidan su, sai naga kakan nawa da kakata duka suna hawaye, yace baiwar Allah dana Aminu yanzun ya kai shekara ishirin da rasuwa!
Dib wuta ta ta dauke, yawun baki na ya kafe na rasa inda zan sanya kaina na zauna na mike, na zauka na kuma mikewa na fara zagaye dakin alamomin tsoro da zautuwa suka bayyana a fuskata dandan dake cikina kanshi harbi na yake daga ciki, tsohuwar nan ta kamoni tana ta nanata innalillahi wa inna ilaihir rajiun sannan bakina ya dauka ina nanatawa, yarnan baki yarda ba? Zo muje kiga kabarin Aminu dan mu a gida muke binne duk wani wanda ya rasu a cikin ahalinmu, na bishi na gane ma idona, tudun kabarin kansa ya baje saboda tsananin dadewa,
duk da haka ban gasgata ba, nace ina son zuwa zaria wurin dangin mahaifiyata, yace ai idan na fita in hau mashin a kaini tasha sai na hau motar zaria, har na mike kuma na tuna bani da ko sisi sai na tsaya, yace ya akayi ne kuma? Nace ai bani da kudi, ya dauko dari ya bani, yace gashi kuma banda kudi kiyi haskuri da darin zata kaiki zarian
Na kamo hannun yarana muka fito daga gidannan a zuciya ta ina fadin ina! Kila dai mahaifina bacewa yayi badai mutuwa ba, yamma lis na iso zaria nayi kwatance nayi kwatance amman babu wanda ya gane unguwar da nake fadi balle sunan wanda nake nema,na gaji da zagaye na dawo bakin wani masallaci na zauna na sanya kuka, yarana ma na ganin haka suma suka saka kuka, wani mutun yazo yana lallashin mu ni da yara, ya dauki salisu yana mashi wasa. Sai wani tsoho ya zo yace Ameera ki dauki yarannan yau komin dare ki kaisu birnin yaro idan ba haka ba yaranki na cikin hadari wani abu zai faru da su idan basu kwana a cen garinba wurin dangin mahaifinsu, ai zunbur na mike kaji abinda tsohonnan yace?
Yarana zasu cutu,mutumen yace ban ga wani tsoho ba,na rike hannun yarana nace ya taimakeni da kudin mota, ya ciro dari biyu ya bani, na hai mashin zuwa bakin titi naira dari, na tsaida mota amman mai motannan yace ni da yarana dari biyar. Na roke shi amman sam yaki yarda sai wani mai mota ya parking ya zo ya biya mana mota ya kuma gaya masa dai dai inda zai aje mu, mun isa birnin yero bayan mangaruba ana aje mu nan naga mijina yana jirana, na ruga ina kuka ina gaya masa yanda mukayi da yan uwan mahaifina, ya bani hakuri yace kawai ki zauna tare da yanuwana, nan nake so yarana su zauna su yi rayuwa, kinga gidanmu cen, kalli ma yayata tana fitowa, ya kwala mata. Kira na waiga na ganta juyowar da zanyi. Naga babu mijina babu alamar shi, nakama hannun yarana nashiga gidan, gidan na laka ne da gane suna cikin kuncin talauci, na shiga na gabatar da kaina, amman su kiri kiri yar 419 suka kirani