sunana Ameerah, bazan iya tantance shekarun haihuwa ta ba, dan bani da takardar haihuwa, amman ina tunanin ba zan wuce shekara ishirin ba!, mu kadai ne a wurin mahaifina, ni da dan uwan tagwaita kata Ameer. Mun taso a wurin mahaifinmu bamu taba ganin mahaifiyar mu ba, baba ne ya raine mu tun muna kanana har girman mu. Mun kasance kullun muna cikin gida, Ameer ne kadai abokin wasa na, bama fita waje kuma baya barin kowa yazo cikin gidan mu.
Mahaifina mutun ne mai wadata domin ban taba neman wani abu na rasa ba tun ina kara mata har girmana, sannan koda yaushe muna tare da mahaifinmu, wuni tare kwana tare, ban taba ganin babana ya je wurin aiki ba, yakan wuni a gida yana wasa da ni da ameer, yakan fita sau daya a rana shima yawanci sai da daddare yake fita, bai dadewa kuma yake dawowa.
Duk da haka bamu rasa komai ba, gidan mu gida ne flat irin na zamani sannan babu abinda babu na jin dadin rayuwa, wuni muke da generator a cikin gidanmu saboda babana ya ce bai yadda da nepa ba, saboda dauke wuta.
idan zaman kadaici ya ishe mu nida ameer mukan matsa ma mahaifin mu ya barmu mu fita, ko mu fita tare, daman dai. Bama wuce kasuwa sayayyar kayan abinci, bayan girman mune mahaifina yake barinmu muje kasuwa mu nida ameer, amman bama fita sai ya daura mana wani dan faren kyalle a hannuwan mu yakan ce waannan kyalle shi zai tsare mu daga sharrin mutun da aljani.
Muna fita zamu ganmu a kan hanya mutane nata hada hadar su ta yau da kullun. Zamuje kasuwa dauke da list din kayan abinci domin mahaifin mu mutun ne mai son cin kayan abincin turawa, baya cin abincin hausawa kwata kwata dan haka nema wasu abubuwan bama rikewa sai an rubuta mana, muna komawa gida kuma bamu kara fitowa sai bayan tsawon lokaci.
A haka muke rayuwar mu har muka girma ni da Ameer. Wata rana. Zaman kadaici ya isheni a gida naje na samu mahaifina na roke shi ya taimaka idan zai fita inda yake zuwa ya je da ni, da kyar ya yadda muka tafi, mun isa wurin da suke taruwa da abokanshi, kowa na zaune sun kewaye wata. Katuwar tukunya abincin da ke ciki nata tafar fasa yana dahuwa amman abin mamaki babu wuta a kasan tunyar, na kasa daurewa sai da na tambayi mahaifina amman matar da ke kula da tukunyar ta dauke ni da mari, sannan ta fara ma mahaifina fada akan me zai kawo bare? Ni dai kawai ya kama hannuna na ganmu a cikin gidaa kuma tun daga ranar ma ya hana mu fita kwata kwata
Tun daga ranar na daina cin duk wani abincin da mahaifina ya girka, sai dai in girka nawa daban na ci. haka muka ci gaba da zama da mahaifina kwata-kwata ya hana mu koda fita kofar gida, ban mantawa akwai ranar da nayi karambani na fita ni kadai ina fitowa kawai na ganni a makabarta ga kaburbura nan birjek da gudu na dawo na fada jikin mahaifina ina shesheka a tsorace na fadi mashi abinda na gani, murmushi kawai yayi ya ce baya hanani fita ba? Kuma ya hana ni fita babu kyallen nan na karo da yake daura mana! Me nene zanyi a wajen wanda babu shi a cikin gida? Ya tashi ya dauko kyallen ya dauraa mani a hannu
ya daura mani kyallen a hannuna ya kuma kama hannuna muka fito waje, a bikin titi na ganmu mutane na ta hada hadar su da suka saba ta yau da kullun muka dan zagaya cikin gari muka koma gida, tun daga ranar ni kaina banyi mafarkin koda kara leke ba balle na ta kaini ga fita. Haka muka ci gaba da zama haar. Na girma, wata rana ina zaune a gida sai ga mahaifina da wani kyakkyawan saurayi sun shigo gida
mahaifina ya kirani ya sanar da ni yayi mani aure ne, saurayin da suka zo tare mai suna Imam shine mijina, kuma anan gidan mu zai zauna da mu dan ba zai yadda ya kai diyarsa inda zata wahala ba, ya bamu daki muka ci gaba da rayuwa aure, na samu cikin na na fari, mahaifina ke kula da ni har na zo haihuwa, sai dai haihuwar tazo da matsala na kasa haihuwa, mahaifina ya fita ya dawo da wani ganye ya shafa mani a saman cikina,
shafa shi ke daa wuya na haifi dan dana namiji, mahaifina shi yayi ungozoma, ya yanke cibi ya je ya binne uwa ya wanke ni da jariri, aka sanya ma yaro suna Auwal, haka na haifi yara na uku duk maza Auwal, Sani da Salisu muna zaman mu lafia da mijina, matsala bata fara aukuwa ba sai da mahaifina ya ce Ameer zai ma aure, anan ne duk asirinsa ya tonu