IBRAHEEMUL KHAWWAS (RAH) yace: "Nayi shekaru goma sha bakwai ina yawo acikin Daji. amma mafi ban-mamakin abinda na gani shine watarana ina cikin tafiya atsakar daji sai na hadu da wani mutum wanda gangar jiki ne kawai. Bashi da Qafafu, babu hannaye, haka yake tafiya yana jan cikinsa akasa.
Sai nayi masa sallama nace "ASSALAMU 'ALAIKA YA BAWAN ALLAH".
Sai yace min "Wa alaikas Salam, Ya kai Ibraheemul Khawwas! ".
Sai nace masa "Yaya akayi kasan sunana, alhali baka ta'ba ganina ba?"
Sai yace "Ai Wanda ya Qaddara zuwanka wannan wajen, shine ya sanar dani sunanka".
Sai nace "Eh hakane. yanzu daga ina kake? kuma ina kake son zuwa?".
Sai yace "Daga Iraqi nake, kuma zan tafi Makkah ne domin gudanar da aikin Hajji"
Da yaga kamar ina mamaki sai yace mun "Ya Ibraheemu shin kana mamakin Mai Karfi ne (wato Allah) wanda yake dauke da wannan rarraunan? ".
Nan na Wuce na barshi. bayan na isa Makkah, Watarana ina Tawafi adakin Ka'aba sai na ga wannan bawan Allah din shima yana tawafi, yana jan cikinsa!!".
Hakikar Nakasasshe shine wanda zuciyarsa ta makance batta ganin gaskiya, Kunnensa ya kurumce ba ya jin gaskiya, Gabobin jikinsa suka kassare bassu yin ibada don neman yardar Allah.