TAMBAYA TA 1566
*******************
Malam nidai ubangiji ya jarabce ni tun ina shekara shida nayi rashin lfy wanda ta sanadin haka na rasa kafafuna bana iya tafiya. Ba inda bamu nimi magani ba amma shuru haka muka hakura muka barwa ubangiji, a haka nayi makaranta primary da secondary. Malam tunda na fara al'ada nake fama da ciwon mara ga fitar farin ruwa ako yaushe wani lokaci kuma ina mafarki, sanna babbar damuwa na yanzu inada shekara 24 amma ba mijin aure ada ina samun masu zuwa amma kwana kadan sai su tafi. Nafi shekara uku ba wanda yazo da sunan yana sona. Sai a fb nake haduwa da mutane su nuna suna sona ina fada musu irin condition danake tare dashi sai su nuna sun amince amma daga baya abinsai ya watse. Ina cikin damuwa sosai ba wani wanda zai taimaka min mallam don ALLAH ka taimakin da shawarwari da addu'a. Nagode.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh. Hakika Allah yakan jarrabi bayinsa ta hanyoyi daban daban. Amma dai duk wanda yayi hakuri kuma ya juya zuwa ga Allah domin neman mafita, to Allah din zai isar masa. Kuma zai yi masa kyakyawar sakayya aduniya da lahira.
Kiyi hakuri ki daure, ki lankwasa zuciyarki zuwa ga bin Allah ako yaushe cikin dare da rana. Akwai mutane da dama daga cikin magabata na kwarai wadanda suka rayu babu hannaye babu Qafafu. kuma ahakan suke bauta ma Allah har suka samu yardarsa suka zama daga cikin manyan Waliyyansa.
Kar ki bar sha'awa irin ta jikinki ta rinjayi sha'awar samun yardar Allah azuciyarki. Kuma kar ki amince ma shaitanun samari su yaudareki don samun biyan bukatunsu ajikinki. Ki yawaita azumi da karatun Alqur'ani da nafilfili da zikirin Allah ako yaushe.
Insha Allahu idan kikaji tsoron Allah, to Allah din zai sanya miki mafita daga kowanne bala'i, kumq zai isar miki bisa dukkan bukatunki na Rayuwar duniya da lahira.
Wannan ruwan da yake fita miki da kuma mafarke mafarken duk suna daga cikin alamomin JINNUL ASHIQ amma babu laifi ki ziyarci cibiyar lafiyar Musulunci mafi kusa domin samun agaji akan wannan.
Ko kuma ki nemi MUHRIQUL JINNI da Almujarrab na ZAUREN FIQHU ki rika amfani dasu. da samu insha Allahu zaki samu waraka da izinin Allah.
fatanmu shine Allah ya yaye miki damuwarki ya kawo miki Miji nagari mai tsoron Allah. wanda nakasarki ba zata zama wata dama agareshi ba. don soyayyar gaskiyar da yake miki.
WALLAHU A'ALAM.