As-salamu alaikum malam barka da himma ubanjigi Allah ya kara maka himma da kwazo ameen
Malam ina neman karin haske ne. Koda yake na riga na aiwatar, malam wata yarinya ce ta kirani tace min dan Allah dan Annabi tana neman alfarma a gareni tace akwai wani abu da tayi min Dan Allah Dan Annabi na yafe mata, nayi nayi ta bayyanar da kanta ko ta gaya min abinda tayi min, taci bayyanar da kanta taci gaya min abinda tayi min, sai tace dan Allah dan Annabi na dai yafe mata, sai ni kuma nayi nazari naga GIRMAN ALLAH DA MONZON SA (SAW) ta rokeni da girman sunayen nan da babu kamarsu daniya da lahira, kuma nasan INNALAHA GAFURUN RAHIMUN ne toh balle ni bil-adam, kuma nayi tunani nayi nazari Ni dai ban san abin da tayi min ba amma ita da tayi abin tayi nadama ta nemi gafara, malam sai nace NA YAFE MATA.
Toh malam ina neman karin haske ne domin watarana ko haka ta tsace faruwa INDA KUSKURE A GYARA MIN
Amma kad a bayyanar da Sunana
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika duk lokacin da 'Dan uwanka musulmi yazo wajenka ya nemi ka yafe masa akan wani laifi da yake tsakaninku, ya kamata ka yafe masa saboda fa'dar Allah (swt) :
"DUK WANDA YAYI AFUWA KUMA YA KYAUTATA, TO LADANSA YANA GA ALLAH".
Awani wajen kuma Allah yace:
"DA MASU HADIYE FUSHI, DA MASU YIN AFUWA GA MUTANE. HAKIKA ALLAH YANA SON MASU KYAUTATAWA".
Kuma Manzon Allah (saww) yace:
"ALLAH BAI QARA MA BAWA KOMAI SABODA AFUWA BA, SAI DAI GIRMA. (ma'ana: indai mutum yayi afuwa, to sakamakonsa awajen Allah shine Qarin girma).
( Sahihu Muslim hadisi na 2,588).
Awani hadisin kuma Manzon Allah (saww) :
"MASU JIN QAI, SUNE KADAI ALLAH YAKE YI MUSU RAHAMA DAGA CIKIN BAYINSA".
Don haka babu laifi akanka, sai dai ma lada mai yawa idan kayi hakuri kayi afuwa ga bayin Allah. kaima Allah zai afuwa gareka kuma zai ji Qanka.
Wallahu a'alam.