Babana yaso Zahra kamar ranshi zai fita, amma rashin fahimtar juna tsakanin magabatansu yasa auren bai yuwu ba.
Zahra anyi mata auren zumunci da dan Gwaggonta Hajiya Kande. Haifuwarsu daya Allah Yayi masa rasuwa. Allah Yasa suna da rabo sai gashi bayan ta gama takaba aurensu yazo ya yuwu da Babana.
Daman Babana yana da mata biyu, Mamarmu ce Uwargida sai Aunty, Mamar su Yasir wanda yake shine sa'a na kuma abokin wasa na.
Babana tsayayyen namiji ne, don haka yana tsaye da matanshi bisa kyakykyawan adalci, kuma su ma sun hada kansu komai na aikin gida, kula da mijinsu da tarbiyyar yara tare su ke yi. Ban taba ganin sun yi fada ba, kuma zuwan Zahra gidan bai canza wannan ba.
Ya kasance kowacce da sashenta a gidanmu, shi ma Baba sashensa daban ne, haka muma yara sashenmu daban. Tunda Amaryar Baba tazo gidan jininmu ya hadu da ita, indai ina gida to tabbas zaka same ni a sashenta, don haka sai Baba yace ya bata ni.
Wata rana na shiga sashen Zahra in fada ma Baba cewar ana mashi sallama a waje, sai na isko Baban zaune tare da Zarah, sun qura ma juna ido, Zarah tana yi masa shagwababben murmushi tare da fari da ido, Babana kuwa ya kasa dauke idonshi daga fuskarta, murmushi yake baki har kunne kamar ba shi ba, ni ban taba ganin irin wannan murmushin a fuskar Baba ba sai yau. Na sulale na koma ban iya qarasawa ba.
Akwai wani lokaci da dukkan yaran gidanmu muka kwashi kwarkwata wajen mai'aikaciyarmu, da yake daki daya muke kwana da ita. Duk da cewa mu mazan an aske mana kawunanmu, amma ni sai inji kaina yana yawan qaiqayi,. Mama Zahra kuwa da ta ga ina sosa kai sai tace da ni "mu ga kan nan naka Khalid?" haka zata yi sosa min tana min danqwashi har barci ya kwashe ni. Ashe Baba duk baya son wannan, rannan ya fito daga cikin daki ya iske ni kai na akan cinyar Mama Zahra tana min susa. Ai kuwa sai ya jefe ni da wata harara: "Wai kai baka jin kunya qato da kai kana irin wannan shagwaba?" Na tashi cikin sauri na bar falon.
"Kai Abu khalid! Susa ce fa kawai nake mashi?"
"To bani so dai, kawai qaton yaro da shi sai..."
Sai naji Mama Gimbiya tayi dariya "Khalid din ne qato? Duka ko shekara sha daya fa bai yi ba? Kai ma dai wata sa'in kamar yaron dai kake Wallahi.."
"Waye yaron?" Sai dai na ji suna guje guje suna ta dariya, Baba na son ya kamata ita kuma tana zulle mashi.
To ire-iren irin haka nayi ta cin karo da su lokacin zaman Mama da Babana.
Mama Zahra ta kasance mai son yara da jan su a jika da yi masu wasanni. A hankali sai duk yaran gidan ya zama falonta ne matattararsu. Haka zata shiga cikinmu muyi duk wani wasa da ita, ga sweets da sauran kayan taba ka lashe kala-kala ta aje domin mu kawai. Bata duka ko yi mana fada, ko laifi mu kayi mata da rarrashi da dubara take ganar da mu kuskurenmu. Kullum sai ta koya mana karatu da addu'o'i. Kuma ta alaqantar mana da yin bismillah akan duk abinda zamu yi.
Wannan yasa nayi ma kaina alqawarin ko min daren dadewa, ba zan auri kowa ba sai salihar mace kuma wacce ta iya soyyayya.
Babanmu na jin dadin irin yadda ta tarbiyyance mu cikin aminci ba bugu ba zagi. Amma su iyayenmu mata basu son haka din, gani suke kamar wani salon qwace miji ne take yi don ya kasance ya fi sonta. Duk da dai basu nuna mata a fili, amma in suka kadaita ba abinda suke yi sai zaginta da gulmarta.
Babana ya tafi wani kwas na wata shidda a qasar Ingila, lokacin suka nuna mata tsangwama qwarai da gaske, a hankali duk suka hana yaran gidan shiga sashenta, sai ni kadai da naqi daina zuwa. Abin mamaki qanwar Baba ce ta basu shawaran su fara bin Malamai don su fitar da ita daga gidan ko kuma ta qasqanta a wajen Baba. Ina jin su lokacin da suke kitsa wannan tsiyar. Na rasa yadda zan yi in sanar da Mama Zahra domin ta hana mu kawo mata gulmar anyi kaza anyi kaza, tana mana nasihan da kullum mu fadi alheri ko muyi shiru.
Amma da naga an fara sa mata surkulle cikin abinci sai nayi ta maza nayi niyyar sanar da ita. Na same ta a cikin quryar daki ta idar da Sallah kenan:
"Mama wani Abu nake so in gaya maki?"
"Menene Khalid? "Kin ga Su Mama da Ant..."
Ban qarasa ba ta rufe min baki tare da yi min hararan nan irin ta fada:
"Ba na hana ka irin wannan ba Khalid? Duk abinda zai haifar da husuma ko qin juna tsakanin musulmi ba wani alfanu yake dashi ba. Kar ka sake irin haka ka ji?"
Na daga kai baki a bude na kasa cewa komi...
Allah sarkii, anya Máma Zarah zata kubuta daga wannan makircin kuwa?
Don jin yanda aka kaya, sai ku biyoni a rubutu na gaba.