Tabbas wannan al'amari ya zama ruwan dare a cikin al'ummar mu. Saboda ana ganin yin hakan shine cikakkiyar wayewa ta zamani wadda fina finai na gida dana waje ke kokarin yadawa, duk ko irin yadda uwaye sukayi tarbiyya wa yayansu cikin qanqanen lokaci zaka samu bulldozer da zata rushe wannan ginin tareda taimakon shaidan (LA), amma dukda haka wasu iyayen suma suna da laifi sosai saboda qauna da so sai su rufe masu ido su kyale yaran babu tsawatawa koda ko sunga wani abu wanda bai dace ba, a idonsu bai zama matsala ba har sae abinda akewa gudu ya faru sai a dawo inda inda, wata rana zakaga uwaye maza suna iya qoqarinsu akan tarbiyar yayansu amma su uwayen mata sai suga kamar an fidda diyansu musamman mata daga cikin tsara da kuma giyar lokaci ma'ana zamani, Sannan su kansu matan na zamani suna da matsala ta kwadayi dason abin duniya da dogon guri, Abinda nake ganin ke qara haddasa wannan barnar rashin qoqarin iyaye su auradda yayansu mata wai har sai kammala jami'a ko makaranta ta gaba da secondary dan gudun mijin ya hana ko kamamanciyar hakan, da kuma maza zakaga yaro yana samun kudi amma iyaye suyi ko oho wajen qoqarin suga sun masa aure, Hanyoyin da iyaye da magabata zasu bi shine su tsawata kuma su saka idanu sosai akan diyansu ko qannensu (mazan da matan) kuma su duqufa wurin yi masu addu'ar tsari, kariya da shiriya. Allah yasa mu gane gaskiya ya bamu ikon binta.
*********************
Malam Siraju, Allah ya saka maka da alkhairi. Allah yasa wadanda akayi dominsu sunji kuma sun amfana..
Lallai akwai babban aiki agabanmu mu iyaye da yayyu. Domin kuwa 'ya'yanmu amanar Allah ce ahannunmu. kuma sai ya tambayemu akan tarbiyyarsu, da komai da komai nasu.