Ya kai 'dan uwana!! ka sani cewa rayuwar nan ta duniya komai tsawonta bata kai wuni guda a lahira ba...
Kada kokarin neman girma ko matsayi ko Mukami yasa ka kauce ma hanyar Allah. Domin kuwa Manyan Sarakuna da masu Mulki da kasaitattun nan na duniya, sune ababen tattakewa aranar lahira.
Kar kwadayin tara kudi da dukiya su sanya ka afka cikin CIN HARAM. Domin kuwa duk jikin da aka ginashi da dukiyar haramun, babu abinda yafi dacewa dashi in banda WUTAR JAHANNAMA.
Dukiyar HALAL ma sai an tambayeka akan kowanne Kobo da Sisin da ka tara.. ta yaya ka sameshi? kuma ta wacce hanyar ka 'batar dashi?
Ita kuwa dukiyar HARAMUN kai tsaye cikin Jahannama zata jefaka.. Ana sanyaka cikin Qabari dukiyarka ta haram zata rikida ta zama Qatuwar Macijiya tazo ta nannade maka wuyanka tana cizonka tana saranka tana cin naman jikinka.. tana ce maka..
"NI CE DUKIYARKA WACCE KA TARA..!! NINE TASKARKA WACCE KA 'BOYE".
Shin ko kasan dubunnan shekarun da zakayi tare da wannan Macijin acikin Qabarinka?? Ko kasan Miliyoyin shekarun da wutar Jahannama zatayi tana babbakar jikinka saboda DUKIYAR HARAM WACCE KA TARA???
Wallahi Rayuwar shekaru 70 ko 80 aduniya acikin Talauci tare da bin Allah da Manzonsa (saww) yafi alkhairi gareka fiye da rayuwar shekaru 70 ko 80 cikin wadata aduniya, tare da yin Wadancan Shekaru marassa adadi acikin Azaba da Uqubah alahira!!!
ZAUREN FIQHU : Na san wadansu zasu karanta wannan sakon, Kuma sun san gaskiya ne, sai dai ba zasuyi aiki dsshi ba, saboda zuciyarsu ta riga ta makance bisa Tsananin Son abinda ba zai amfanesu ba...
Wannan ba labari bane, ba tatsuniya bace.. A'a tsantsar Gaskiya ce wacce kowannenmu sai ya risketa idan bai kiyaye ba!!
DAGA ZAUREN FIQHU