Akwai mutane da dama wadanda zasu shiga wuta ne bisa dalilin QASKANTAR DA LAIFI AWAJEN ALLAH. wato laifinsu shine suna aikata Zunubi amma basu ganin girmansa ballantana suyi nadama su tuba zuwa ga Allah.
Hakika shi Allah BABBAN SARKI NE wanda shi ya halicci kowa da komai. Kuma yana son bayinsa su girmamashi su san cewa Shine Ubangijinsu. Kamar yadda yake so su gode masa idan yayi ni'ima agaresu..
Abdullahi Ibnul Mubarak watarana yaga wani saurayi yana tsugunne awani waje yana ta kuka, jikinsa yana girgiza... Bisa dukkan alamu yana cikin tashin hankali.
Sai ya tambayeshi Menene dalili?? Sai yace "NA TA'BA YIN GULMAR WANI MUTUM NE AWANNAN WAJEN.. SHI YASA KULLUM IDAN NAZO WUCEWA TA WAJEN NAN SAI NA TUNO DA WANNAN LAIFIN DANA AIKATA SAI TSORO YA KAMANI. INA TUNANIN TSAIWAR DA ZANYI AGABAN ALLAH DOMIN AMSAR SAKAMAKONA!!".
Allahu Akbar!!! Sai shima Ibnul Mubarak ya fashe da kuka, suka zauna sukayi ta kuka tare don tsoron Allah!!
Shin kai yanzu laifuka nawa kake aikatawa kullum awajen zamanka, ko awajen aikinka, ko awajen kasuwancinka??
Acikin Zunubi babu wani Qarami domin kuwa komai Qankantarsa zai iya hallakar dakai. Shi yasa ma Manzon Allah (saww) yace : "MUTUM YAKAN FURTA WATA KALMA WACCE YAKE GANINTA KAMAR BA KOMAI BA, BWI DAMU DA ITA BA.. AMMA ITA ZATA AFKAR DASHI ACIKIN WUTA".
Yana daga cikin Makircin Iblis (L. A) idan ka aikata zunubi sai ya Qaskantar maka da girman laifin a zuciyarka, kuma ya mantar da kai hanyar tuba, ya jefa maka Shagaltuwa acikin ranka.
Kana nan sai mutuwa ta riskeka ba tare da ka tuba ba.. Don haka ya kamata mu zama ko yaushe cikin neman gafarar Allah da tuba agareshi. mu dena sakankancewa.
Ya Allah ka gafarta mana.