Ya zama wajibi Iyaye su Qara sanya ido akan harkokin 'Ya'yansu Mata. Musamman wadanda suka balaga.
Amatsayinka na Uba, ka sanya ido akan irin Qawayen da 'yarka take yawo dasu. Ka san daga ina suke, daga wanne gida, yaya iyayensu suke.. Kuma menene yake kawosu wajen 'yarka!
Idan ka barsu Kara-zube, kana nan zaka ga irin ta'adin da zasu janyo maka. Watakil su rika jan 'yarka zuwa wajen Party da samari, ko kuma su koya mata wata mummunar dabi'ar Zina ko madigo da sauransu.
Miyagun Qawaye sun taka rawa sosai wajen lalacewar tarbiyyar Mafiya yawan 'yan matan da suka lalace azamanin nan. Kuma ayawancin lokuta su suke kangarar da 'ya'yan mutane.
Mafiya yawan 'yan matan yanzu sunfi mutunta shawarar da Qawayensu suke basu fiye da shawarar da ta fito daga bakin iyaye ko 'yan uwa.
Hakanan Miyagun Qawaye suna taka rawa wajen mutuwar auren wasu matayen marassa tunani. Kin kwashe sirrin Mijinki kin gaya ma Qawarki, ita kuma dama tana jin haushin kin rigata samun Miji, ko kuma Mijinta bai kai naki ba. Don haka ba zata baki shawara mai kyau ba. Da zarar kin bi shawarwarinta shikenan sai abu ya Qara kwabewa, daga karshe kiyi asarar aurenki.
Wata kuma Qawar ta riga ta fara zina. Don haka bata da samari sai mazinata. da zarar kin fara yawo da ita sai ta hadaki da abokin saurayinta. watakil shima mazinacin ne. Idan kika Qi basu hadin kai, ita Qawar taki ce zata janyo hankalinki tace miki ai wannan ba komai bane.
Iyaye da manyan Yayu, ya zama wajibi mu kiyaye amanar da Allah ya dora mana mu matsa sosai wajen tarbiyyar 'ya'yanmu mata da Qannenmu. Koda jama'a zasu ga laifinmu.
BISSALAM.