Yana daga cikin Makircinsa shi Iblees yakan sanya ma mutum kokonto acikin samuwar Ubangiji. idan ya samu nasara kuma daga nan sai ya janyoshi zuwa ga kafirci. Ga wani misali nan kamar haka:
IBNU UMAR (ra) YACE:
"Muna Zaune tare da Manzon Allah (saww) watarana, sai ga Wani Tsoho mai mummunar siffa, mai yagaggun sutura, Mai doyin jiki kamar Mushe, Ya shigo wajen, Ya ratso cikin Jama'a, yana tattaka wuyan Mutane, yana tutture kafadunsu, har sai da yazo ya zauna agaban Manzon Allah (saww).
Sai yace wa Manzon Allah (saww): "Waye ya Halicceka?"
Sai Manzon (saww) yace masa: "ALLAH NE"
Sai yace: "Waye ya Halicci Sammai?" Sai Manzo (saww) yace Masa "ALLAH NE"
Sai yace: "Waye ya halicci Qassai?" Sai Manzo (saww) yace masa "ALLAH NE"
Budar bakin Mutumin nan sai yace: "TO SHI ALLAH DIN WAYE YA HALICCESHI?"
Jin wannan Kalamin sai Manzon Allah (saww) yace: "SUBHANALLAH!"
Sai ya rike goshinsa, ya Sunkuyar da kansa Qas, Shi kuwa wannan Tsohon sai ya tashi ya fita.
Da Manzon Allah (saww) ya cira Kansa sai yace: "KU KAMO MIN MUTUMIN NAN!"
Da muka fita nemansa, mukayi ta dubawa bamu ganshi ba. Sai Manzon Allah (saww) yace:
"IBLEES NE YAZO DOMIN YA SA MUKU KOKWANTO ACIKIN ADDININKU"
* IMAM AL-BAIHAQY ne ya ruwaitoshi acikin DALA'ILUN NUBUWWAH, juzu'I na 7 shafi na 125. Daga Sayyiduna ABDULLAHI bn UMAR (ra).
* Ibnu Hibban da Abu Zur'ah sun inganta shi.
Lallai Shaitan rashin mutuncinsa ya kai Kololuwa, kuma Qiyayyarsa garemu ta wuce iyaka!! Tunda yaje har gaban Shugaban Halittun Allah baki daya, domin ya dulmiyar da al'ummar Musulmai.
DAGA ZAUREN FIQHU