1. Bawa yaro nono a kwance
2. Sawa yaro suna mara kyau
3. Barin yaro da kazanta.
4. Rashin jan yaro a jika.
5. Kin ciki idan ya shiga.
6. Rashin nemawa yara iyaye nagari.
7. Sabawa ka’idojin shari’a a wurin saduwa.
8. Yawan bacin rai da tashin hankali ga uwa yayin da take da ciki.
9. Rashin aikata ladduba da sharia ta shinfida da zarar an haifi yaro.
10. Daukar yaro, ko bashi nono duk lokacin da yayi kuka.
11. Rashin tsara lokacin shayarwa.
12. Wuce ka’idar lokacin daya dace a shayar da yaro.
13. Rashin sawa yaro tsoron Allah a zuci sai na iyaye.
14. Fifita wani a tsakanin ‘yaya.
15. Daurewa yaro gindi in yayi laifi ko tsokana.
16. Bawa yaro ko sayamasa duk abinda yanema.
17. Rashin koyawa yaro shiga irin ta musulunci.
18. Rashin kai zuciya nesa in yaro yayi laifi.
19. Rashin koyawa yaro yanda zaiyi Magana da nagaba dashi.
20. Rashin sanin gurin da yaro yake zuwa idan yafita.
21. Rashin sa yaro a makarantar data dace.
22. Rashin koyawa yaro yadda zai karbi bako.
23. Sayawa yaro kayan wasan da basu daceba.
24. Sawa yaro abinci yai taci ba iyaka.
25. Koyawa yaro mummunar shiga ta hanyar shigar da iyaye sukeyi.
26. Rashin karantar halin yaro dayi masa hukunci da daya daga cikin halayen ‘yan uwansa.
27. Tilastawa yaro yayi abinda bazai iyaba.
28. Zabawa yaro fannin dazai karanta alhali bashi yake soba, ko bazai iya yinsaba.
29. Yawan zagi da iyaye sukeyi a gaban yaro.
30. Hana yaro yin wasa alokacinsa.
31. Sanya fina finai marasa kyau, Yaro yana gani.
32. Yiwa ‘yaya auren dole.
33. Rashin manufa daya tsakanin iyaye.
34. Hora yaro ta hanyar hanashi abinci, ko barinsa da yinwa, bayan da akwai abincin da za’a bashi.
35. Bawa yaro umarni da yabawa juna.
36. Barin yara maza da mata suna cudanyar data sabawa shari’a.
37. Barin yara suna zuwa bukukuwa barkatai.
38. Dorawa yara maza ko mata talla.
39. Rashin yiwa yara bayanin sabon yanayin da zasu fuskanta idan sun kusa balaga.
40. Kin tsayarwa da yarinya manemi daya, da barinta tana harka da samari barkatai.
41. Barin yarinya ace sai takawo miji dakanta sannan za’a yimata aure.
42. Barin ‘ya mace ta dade tana karatu, kamar tagama jami’a batare da miji ko wani tsayaiyen manemiba.
43. Nunawa yarinya ko yaro cewa aure yana hana karatu.
44. Rashin kyakkwawar manufa gurin neman aure.
45. Yawan dukan yaro, ko duka ba a bisa ka’idaba, ko daukar duka abisa sahun farko na hora yaro.
46. Kyale yaro idan yanata zaro
Magana barkatai.
47. Yiwa uwa fada, ko cin zarafin miji a gaban ‘yaya.
48. Yiwa yaro fada agaban ‘yan uwansa.
49. Rashin daukar matakin daya dace idan yaro yayi laifi.
50. Rashin koyawa yaro tattali.
Wadannan sune abubuwa guda 50 da suke lalata tarbiyyar yaro.
Da fatan zamuyi aiki da wannan nasiha.