BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugaban dukkan Annabawa da Manzanni, Annabi Muhammadu tare da dukkan iyalan gidansa masu albarka, da Sahabbansa yardaddu.
Wannan shine darasi na bakwai acikin karatunmu na Kitabul Kaba'ir. wanda muke gabatarwa a Zaurukanmu na Whatsapp
Kamar yadda aka sani, har yanzu muna magana ne akan laifin mutanen da suke tozartar da sallah.
Wadanda basu yinta akan lokaci, ko kuma suna jinkirta yinta har lokacinta ya Qure, ko kuma irin mutanen nan wadanda suna yin sallah amma hankalinsu baya cikin sallar.. Ko kuma mutanen da suke yinta cikin jahilci.. Basu san abinda yake gyarata ba, ballantana wanda yake 'bata ta. Kuma girman kai ya hanasu suje wajen Malaman Zaure masu karantar da litattafan ilimi su koyi yadda zasuyi ibadah.
Akwai wani hadisi da aka ruwaito cewa Manzon Allah (saww) watarana yace ma Sahabbansa (Allah shi yarda dasu) "YA ALLAH KAR KA BAR SHAQIYYI ACIKINMU KO KUMA MAHRUMI (WANDA AKA HATAMTAWA SHIGA ALJANNAH).
Sannan sai ya tambayesu "SHIN KO KUN SAN WANENE SHAKIYYI, (WANDA YA TA'BE) KUMA MAHRUMI (WANDA AKA HARAMTA MASA SAMUN RAHAMA)?"
Sai suka ce "Wanene wannan Ya Rasulallahi? ". Sai yace "WANDA YAKE BARIN SALLAH".
Kuma an ruwaito cewa farkon wadanda za'a BAQANTA fuskokinsu aranar ALKIYAMA, sune masu barin sallah. Kuma cewa acikin Jahannama akwai wani Wagegen rami wanda ake kiransa da suna "MULAHHAM".
Acikinsa akwai zabga-zabgan Macizai. Kowacce Macijiya kaurinta ya kai kamar kaurin Wuyan babban Rakumi. Kuma tsawonta ya kai kamar tsawon tafiyar wata guda.
Wadannan Macizan zasu rika Cizo da saran masu laifin wasa da sallah.. Har sai guba da dafin cizon Macijiyar ya game jikinsu tsawon shekaru saba'in, sannan naman Jikinsu ya rube, ya zube (Ya Allah ka tsaremu don alfarmar Ma'aiki saww)
* GA WATA HIKAYA (LABARI) MAI BAN-TSORO!! :
"Wata mata daga cikin Banu Isra'eela tazo wajen Annabi Musa (as) tace masa: "Ya Ma'aikin Allah, ni na aikata wani Zunubi mai girma. Amma na tuba zuwa ga Allah. Shine nazo gareka don ka roka min Allah ya gafarta min zunubaina, kuma ya karbi tubana.
Sai Annabi Musa (as) ya tambayeta "SHIN MENENE ZUNUBIN NAKI?".
Sai tace "Ni nayi Zina ne, har na haifi yaro da wannan zinar, sannan na kashe yaron!!".
Daga jin haka sai Annabi Musa (as) yace mata "FITA DAGA NAN YA KE FAJIRA! KADA SHU'UMANCINKI YASA WUTA TA SAUKO DAGA SAMA TA QONEMU GABA DAYANMU!".
Sai ta fita daga gareshi zuciyarta ta karaya.
Sai ga Mala'ika Jibreelu (as) ya sauko da wahayi zuwa ga Annabi Musa (as) yace masa
"Ya kai Musa! Ubangiji (SWT) yace maka "YA KAI MUSA, MAI YASA KA KORI WANNAN BAIWAR ALLAH WACCE TA RIGA TA TUBA?
SHIN BAKA SAMU WANDA YAFI SHARRI FIYE DA ITA BANE?"
Sai Annabi Musa yace "Ya Jibreelu wanene yafi ta sharri?"
Sai yace "MASU BARIN SALLAH DA GANGAN DON GANGANCI".
* Ga wata Hikayar itama mai BAN-TSORO!!
Wani daga cikin Magabata na kwarai, yana da wata 'yar uwa wacce ta rasu. Yayin da aka je za'a binneta, sai jakar kudinsa ta fada cikin ramin Qabarin. Amma babu wanda ya gani (sai shi kadai).
Har sai da ya dawo daga wajen Qabarin nata sannan ya tuna. Don haka ya koma ya bude Qabarin (domin ya dauki kudinsa).
Kawai sai ya tarar Qabarin yana balbala mata WUTA!!..
Don haka sai ya mayar mata da Qasar akanta sannan ya dawo wajen mahaifiyarsu cikin bakin ciki, yana kuka.. Yace mata "Ya ke mahaifiyata, ina so ki ban labari akan 'yar uwan nan tawa, shin menene ya kasance tana aikatawa?"
Sai tace "Mai yasa kake tambaya akanta?"
Sai yace "Ya Uwata! naga Qabarinta ne yana balbala mata Wuta".
Sai mahaifiyar tasu ta fashe da kuka sannan tace masa "'Yar uwarka ta kasance tana Wulakanta sallah, tana jinkirtar da ita bisa lokacinta".
Indai wannan shine yanayin mai jinkirta sallah, to yaya kuma wadanda basu yinta da gangan!!
Ya Allah ka taimakemu kasa mu kiyayeta mu rika yinta tun a farkon lokacinta. Kai ne mai kyauta, mai baiwa, mai karamci.
YANZU KUMA ZAMUYI MAGANA AKAN UKUBAR DA ZA'AYI MA MUTANEN DA SUKE TAUYE SALLAH, BASU CIKA RUKU'IN DA SUJUDARTA.
Acikin tafseerin ayar nan ta cikin Suratul Ma'un in da Allah yake cewa "RAMIN AZABA YA TABBATA GA MASU SALLAH. WADANDA SUKE RAFKANUWA DAGA BARIN SALLARSU".
Wadansu Malaman sun ce ana nufin mutumin da yake guggufiya a sallarsa, ba ya cika ruku'inta da sujjadarta.
Anan zamu tsaya insha Allahu sai a karatu na gaba zamu dora daga kan inda muka tsaya.
Da fatan Allah ya taimakemu akan shaitan da kuma zuciyoyinmu, ya bamu nasarar zama cikin bayinsa nagartattu don falalarsa da rahamarsa.