Assalamu alaikum wa rahmatullah, mallam yaya kowa da komai?
Mallam don Allah irin wanda iyayen su suke zuwa wajen malaman tsubbu ko bokaye ya hallatta 'yayan su su dinga basu kudi tunda sun san in sun basu za su iya kai ma malaman? Kuma mallam in iyayen suka kawo musu wani magani ko wani abu su yi anfani da shi daga wajen malaman suka qi yi har ran iyayen ya baci suna da laifi?
(Daga wata baiwar Allah)
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hakika Allah ya wajabta ma 'ya'ya suyi biyayya ga iyayensu. A inda yake cewa:
"UBANGIJINKA YA WAJABTA CEWA KAR KA BAUTA MA KOWA SAI SHI. KUMA KA KYAUTATA MA IYAYE".
(Suratul Isra'i).
Awanu wajen kuma yace : "KA GODE MIN, KUMA KA GODE MA IYAYENKA".
Amma Ubangiji ya sanya mana iyakar godiya da kuma biyayyar da zamuyi musu. A inda yake cewa:
"AMMA IDAN SUKAYI JAYAYYA DA KAI (SUNA KIRANKA CEWA) KAYI SHIRKA DANI, DA WANI ABU WANDA BAKA DA ILIMI AKANSA,TO KAR KAYI MUSU BIYAYYA".
Da wannan dalilin ne malamai suka ce bqi halatta 'Ya'ya suyi ma iyayensu biyayya cikin abinda ya zamto sabon Allah ba.
Manzon Allah (saww) yace : "BABU BIYAYYA GA DUK WANI MAHALUKI CIKIN SA'BA MA MAHALICCI".
Wato ba zaka yiwa wani mahaluki biyayya ku sa'ba ma Allah ba.
Wajibi ne 'ya'ya su taimaka ma iyayensu da kudaden kashewa don biyan bukatunsu na yau da kullum. Amma in dai suka umurceka cewa ka basu kudi zasu je wajen BOKAYE, to bai halatta ka basu ba..
Hakanan idan suka karbo maganin awajen bokaye ko matsafa, suka ce kayi amfani dashi. To bai halatta kayi amfani dashi.
Ki karba ki watsar ba tare da saninsu ba. Kuma kici gaba da yi mudu addu'a tare da wa'azi da nasihohi cikin kalmomi masu kyau.
Ki nuna musu cewa Allah ya hana wannan abinda suke yi. Kuma Manzon Allah (saww) yace Duk wanda yaje wajen boka ko 'dan buda, kuma ya gaskatashi akan abinda ya fada masa, to hakika ya kafirce ma dukkan abinda Annabi Muhammadu (saww) yazo dashi.
Ya Allah ka shiryi masu yi.
WALLAHU A'ALAM.