Yau naga wani hoto wanda ya 'daga min hankali... wasu Daliban ZAUREN FIQHU WHATSAPP ne suka turo min daga garuruwa daban-daban, amma duk dai hotunan iri guda ne.
Wani saurayi ne da budurwarsa suka dauki hotunan kala-kala. Kuma abisa Mummunar sifa irin ta FASIKANCI DA RASHIN IMANI Acikin hoto na farko Sun rungume juna, ita ta rungume Qirjinsa da nata, shi kuma ya rike Qugunta..
A Hoto na biyu kuwa, Sun hada fuskokinsu waje guda, Sun zaro harsunansu. Shi yana tsotson harshenta itama tana tsotson harshensa...
Wallahi hankalina ya tashi. Domin ni dai wallahi ban taba ganin koda Inyamurai sun aikata irin wannan ba, ballantana 'ya'yan Hausawa, Saurayi da budurwa!!
Wallahi wannan ba Qaramar Qazanta bace!! Ta yaya za'a samu Zuriyya masu kunya, masu mutunci a irin wannan auren idan an yishi??
Babban abinda ake bukata arayuwa shine Albarka. Kuma ba'a samun albarka sai ta hanyar bin Allah, da jin tsoronsa afili da boye.
Wadannan hotunan da samari da 'yan mata suke dauka, abu ne wanda yake nuna tsananin rashin Tsoron Allah afili, sannan kuma yake Qara fito da Fasikancinsu da fajitcinsu a idon duniya.
Wallahi duk wanda bai ji kunyar Allah ba, to Allah ma ba zai ji kunyarsa ba. Kuma Duk wanda yake bayyan ayyukan sa'bon Allah afili irin wannan, to alama da take nuna cewa yana daga cikin wadanda Allah da Mala'ikunsa suke tsine musu!!
Ya Allah ka kiyayemu daga aikata zina da duk dangoginta.