Hana Buhari yin takara, cire Jega daga shugabancin INEC
Bayan samun nasarar tursasa tare da matsa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta daga ranakun gudanar da zabuka masu zuwa da sati shida, da fadar shugaban kasa da jam’iyyar PDP suka yi ta amfani da hukumomin tsaro na sojoji dana ‘yan sanda, yanzu kuma boyayyiyar manufar su ta daga zabukan ta fito fili.
Wani rahoto da jaridar Vanguard ta fitar a yau, na nuna cewa a yanzu PDP manyan kudirorin su biyu, na farko su bi duk halin da ya kamata na ganin sun yi amfani da kotu an hana Janar Muhammadu Buhari na APC yin takara, ta hanyar cewa ba shi da takardun kammala sakandare.
Kudiri na biyu kuma shi ne su tursasa Shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ajiye mukamin sa ko kuma su yi masa murabus ta kowane hali, saboda a cewar gwamnati a yanzu sun kasa gane ina ne gaban Jegan ya dosa, tare da zarginsa da hada baki da manyan Arewa don maida mulki yankin.
A jiya #HAUSA24 ta samu wani rahoton sirri da yake nuna cewa fadar shugaban kasan ta samar da wani alkali na bogi tare da bashi ladan naira bilyan 2, don ya gudanar da shari’ar da za ta hana Janar Buharin yin takara.
A bangaren Jega kuma tuni har an fitar da sunan wani Farfesa dan uwan gwamnan jihar Ondo da zai zama sabon shugaban hukumar ta INEC, wanda majiyar mu ta bayyana cewa yana da alaka ta kusa da jam’iyyar ta PDP.
“Sati shida ya isa kotu ta samu damar fito da hujjojin da za tayi amfani da su kan Buhari ta hana shi yin takara. Haka lokacin ya isa a shirya komai akan Jegan da tantance sabon shugaban da zai gaje shi” in ji majiyar jaridar ta Vanguard.
Sai dai masana harkokin siyasar kasar nan, na ganin cewa daukar irin wadannan haramtattun matakai a halin da siyasa take a kasar nan a yanzu zai iya haifar da rikicin kabilanci ko na bangaranci da zai iya kaiwa ga rugujewar kasar baki daya.
source hausa24.com
Title :
GASKIYA TA BAYYANA: Babban Dalilin Daga Zabuka Masu Zuwa
Description : Hana Buhari yin takara, cire Jega daga shugabancin INEC Bayan samun nasarar tursasa tare da matsa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta da...
Rating :
5