Hukumar zaben Nigeria ta bayyana wasu tsare-tsare a kan yadda
wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu za su kada kuri'a a
babban zaben kasar da ke tafe.
Al'ummar jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa su ne wadanda
tashin hankalin ya fi shafa.
Shugaban INEC, Furofesa Attahiru Jega ya ce 'yan gudun hijrar da ba
su bar jihohinsu ba ne kawai za su samu damar yin zaben.
Sai dai kuma, an tashi daga taron ba tare da samun cikakken bayani
kan yanayin tsaro yayin zaben ba, musamman a jihohin Borno da
Yobe da kuma Adamawa inda rikicin Boko Haram din ya fi kamari.
Hukumar agajin gaggawa ta Nigeria, NEMA ta ce mutane kusan
miliyan daya ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram.
Source bbchausa
Title :
'Yan gudun hijira za su yi zabe - INEC
Description : Hukumar zaben Nigeria ta bayyana wasu tsare-tsare a kan yadda wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu za su kada kuri'a a babb...
Rating :
5