Jagoran kungoyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin daukar alhakin kai mumuman hare-haren garin Baga da Doron Baga a Jihar Borno da ke arewa maso gabacin Najeriya, tareda yin barazana ga wasu kasashen dake makoftaka da Nigeria. Abubacar Shekau wanda ke bayana hakan a cikin wani sabon sakon bidiyo da aka wallafa a shafin internet na youtube ya yi barazanar kaddamar da hare hare a kasashen Nijar da Kamaru da Chadi duk makwabtaka Najeriya. Wanan dai shine karo farko da Shugaban Boko Haram ya nuna yatsa ga Niger inda ya gargadi Shugaban wanan kasa Mahamadou Issufu akan ziyarar da ya kai Faransa bayan harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo da ta sake yin zanen batanci ga annabi Muhamed (SAW). Wanan na zuwa a daidai locacin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya suka gudanar da wani taro a Nijar domin tattauna barazanar kungiyar da ke ci gaba da zama babbar barazana ga Yankin.
Title :
Abubakar Shekau Yayiwa Kasashen Niger, Chadi da Kamaru Barazana
Description : Jagoran kungoyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin daukar alhakin kai mumuman hare-haren garin Baga da Doron Baga a Jihar Borno da k...
Rating :
5