Kan Laifin Karkatar Da Kayan Tallafin Da Aka Ba Shi Ya Rabawa Al'ummarsa
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma sauraron korafe korafe ta jihar Kano, ta tsare shugaban karamar hukumar Kumbotso Alhaji Kabiru Ado Panshekara, bisa tuhumar da amfani da karfin kujerarsa wajen karkatar da tallafin kayan masarufin gwamnati na ragewa jama’a radadin dokar hana su fita saboda annobar coronavirus.
Shugaban hukumar yakar cin hancin da rashawar ta Kano Muhyi Magaji Rimingado ya tabbatar da kamen da suka yiwa Kabiru Ado Panshekara a yau asabar, kamar yadda jaridar Solacebase dake birnin na Kano ta tabbatar.
Muhuyi Magaji yace hujjoji sun bayyana yadda shugaban karamar hukumar ta Panshekara ya karkatar da kayayyakin abincin da aka mika masa don tallafawa marasa karfi, ta hanyar rabar dasu ga jami’an tsaron da suka hada da na ‘Yan Sanda, DSS da, jami’an kula da shige da fice wato Immigration a turance, sai kuma wasu jami’an hukumar Hisbah, abinda ya sabawa sashi na 22, da 23 da kuma 26 dake karkashin dokar 2008 da ta kafa hukumar sauraron korafe korafen al’umma da yakar cin hanci da Rashawar ta Kano.
Daga Shafin Rariya
Title :
An Kama Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Dake Kano,
Description : Kan Laifin Karkatar Da Kayan Tallafin Da Aka Ba Shi Ya Rabawa Al'ummarsa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma sauraro...
Rating :
5