Ministar harkokin mata ta Najeriya, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.
Ministar harkokin mata ta Najeriya, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.
"Kowa yasan da sanin cewa nice na lashe zaben gwamnan jihar nan a shekarar 2015, har babbar jam'iyyar adawa ma ta PDP ta shaida cewar nice na lashe zaben, saboda haka zan sake tsayawa takara a zabe mai zuwa inda har Allah yasa ina raye.
"Na san da cewa komai iko ne na Allah, na san Allah ne bai nufe ni da zama gwamnan jihar nan ba. Na lashe zaben 2015, amma Allah bai so na hau kujerar gwamnan ba. Zan cigaba da yarda da nufin Allah da kuma cigaba da zama tare da mutanen jihar Taraba, kuma na san idan har Allah yaso zan lashe zaben 2019," inji ta.
Source :naij hausa
Title :
Zan Sake Neman Gwamnan Taraba - Aisha Alhassan
Description : Ministar harkokin mata ta Najeriya, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai g...
Rating :
5