Sanannen Malamin addinin Islama dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi ya bayyana bacin ransa gami da damuwa game da yadda hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta wulakanta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Malamin ya bara ne a yayin gabatar da tafsirin Al-Qur’ani kamar yadda ya saba yi a watan Ramadan, inda yace EFCC ba ta da hurumin bayyana mutum a matsayin mai laifi, don haka bai kamata su yi ma Ramalan abinda suka yi masa ba.
A cikin bayanin Malamin ya bayyana cewa yaso ace Ramalan bai baiwa EFCC hadin kai ba, “Dama an dauke shi ne yana fada dasu akan bai yarda ba, wannan shi yafi.
” Inji Malamin.Gumi bai karkare jawabinsa ba har sai da ya bayyana bacin ransa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda da ana bin laifi da Buhari bai zama shugaban kasa ba.
“Mutanen Kudu sun yi hannu riga da gwamnatin nan, Mutanen Arewa ne kawai suke binsa, dakikan mutane, a auna Buhari da tsohon shugaban kasa Shagari a gani wanene ya ci kudin gwamnati?” Inji Dakta Gumi.
Source :naij hausa
Title :
Yan Arewa Dakikai Ne, Yan Kudu Kuma Basu Tareda Buhari - Sheikh Gumi
Description : Sanannen Malamin addinin Islama dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi ya bayyana bacin ransa gami da damuwa game da yadda huk...
Rating :
5